31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Yobe ta Arewa: Lauyan Machina ya yaba wa alkali ga me da hukuncin da aka yanke

LabaraiYobe ta Arewa: Lauyan Machina ya yaba wa alkali ga me da hukuncin da aka yanke
Machina
Kotu ta bayyana Machina a matsayin sahihin ɗan takarar Sanatan APC a Yobe ta Arewa

Lauyan dan takarar kujerar Sanatan jihar Yobe a karkashin jam’iyyar APC, Ibrahim Bashir Machina, ya yaba hukuncin da kotu ta yanke na bayyana wanda yake karewa a matsayin wanda ya ci takarar gundumar yobe ta Arewa .

Mista Bawa ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba a harabar kotun cewa hukuncin da Fadima Aminu, mai shari’a ta yanke, ya karfafa masa gwiwa ga tsarin shari’ar Najeriya.

Mista Machina dai ya garzaya kotu ne domin neman a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na APC a Yobe ta Arewa wanda aka gudanar a ranar 25 ga watan Mayu.

Ya kuma bukaci kotun da ta tilasta wa jam’iyyarsa ta aika sunansa zuwa ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a matsayin dan takararta sannan kuma ya nemi hukumar INEC ta buga sunansa a cikin jerin sunayen ‘yan takarar da za su tsaya takara a zaben majalisar dokoki ta kasa a shekara mai zuwa.

Sai dai Shugabannin jam’iyyar APC sun aike da sunan shugaban majalisar dattawa mai ci, Ahmad Lawan, a matsayin dan takararta.

Mista Lawan bai shiga zaben fidda gwani da INEC ta gudanar ba a ranar 25 ga watan Mayu.

In ba a manta ba Mista Lawan ya fafata a zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar APC. Amma sai dai bai yi nasarar samun tikitin ba,wanda hakan ya sa shugabannin jam’iyyar suka sanya sunan shi a matsayin dan takarar jam’iyyar a gundumar da yake wakilta a majalisar dattawa tun shekarar 2007.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe