Ma’abota amfani da manhajar TikTok sun yi caa akan wata mata wacce ta ajiye wa mijinta faranti babu komai a cikinsa. A bidiyon an ga yadda mijin ya zauna yana jiran abinci sai ta kawo masa faranti a rufe ashe babu komai cikinsa, Legit.ng ta ruwaito.
A cewar matar, mijin yana damunta da ta kawo masa abinci ba tare da ya fita ya yi aikin fari balle na baki ba.
Ma’abota amfani da TikTok sun yi tsokaci karkashin bidiyon wanda wasu ke ganin zolayarsa take yi yayin da wasu ke kallon hakan a matsayin cin mutunci.
Ga wasu daga cikin tsokacin:
@user6042534519611 tace:
“Ki bada masa yaji.”
@tracyabnandem tace:
“Ki bashi cokali mai yatsu da yaji da miya.”
@rose_pro6 tace:
“Tabbas duk namijin da ba ya aiki bai cancanci a bashi abinci ba.”
Wata kuma tace:
“Ni ban damu ba don miji ba ya aiki, wanda dai ya zauna ne hankalinsa kwance ke bata min rai.”
@19ray60 yace:
“Bai dace ma sai an matsa wa namiji zai nemi abinyi ba.”
Edafe Endurance tace:
“Ya zauna yana jiran abinci mai kyau da ruwa.”
Magidanci na son amsar hotunan tsiraicin tsohuwar matarsa don ya dinga tunawa da ita
Wata mata daga Utah, can Amurka ta bayyana yadda wani Alkali ya umarceta da ta bai wa tsohon mijinta albam din hotunan tsiraicinta a matsayin daya daga cikin abubuwan da ya bukata don ya sake ta, LIB ta ruwaito.
Sai dai a cewar Lindsay Marsh, ta taba yin hotunan ne a farkon aurensu inda ta hada masa da kalamai masu dadi na soyayya a albam din. A watan Afirilun 2021 bayan kwashe shekaru 25 da aurensu, tsohon mijinnata ya bukaci ta bar masa albam din hotunan don ya dinga tunawa da ita.
A cewarta, kawai wannan shirin tozartata da wulakanta ta aka yi. Ta bayyana cewa ya labarta yadda su ka yi ne ga mutane don su ji su hankalta don gudun fadawa makamancin yanayin da take ciki a halin yanzu.
A cewar Marsh, ta yi mamaki akan yadda mijin nata ya nemi wannan albam din yanzu da suke shirin rabuwa. Sai dai Alkalin, Micheal Edwards, mai zama a 2nd district court, ya bi bayan tsohon mijin nata.
Alkalin ya bukaci ta mayarwa asalin wanda ya dauketa hoton don ya cire duk inda jikinta ya fito a albam din. Bayan Marsh ta je wurin mai hoton, ya ba zai iya yin hakan ba. Ganin haka Alkalin ya bukaci ta bai wa wani mai hoton na daban don ya cireta a hotunan.
Kamar yadda Alkalin ya bukata, duk wanda zai gyara hotunan zai ga inda ta bayyana da kamfai da rigar mama ko kuma wanda babu komai a jikinta sannan ya cireta a ciki.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com