Wata bokanya mai suna Ajefunke3 a TikTok ta dauki tsatstsauran mataki bayan ‘yan sanda sun kama wasu makadanta. A wani bidiyo da ya dinga yawo, ta bayyana wata ta yi tsafe-tsafenta a wurin wani tafki yayin da ‘yan sanda su ka kama mata makada, Legit.ng ta ruwaito.
A cewarta, bayan sun kama makadan, ta tattaro makadanta inda su ka afka ofishin ‘yan sanda don su samo mutane. Ta ce wajibi ne jami’an su gane kurensu akan mummunan aikin da su ka yi mata.
Kamar yadda ta bayyana da harshen yarabanci:
“Kun ganni nan a ofishin ‘yan sanda. Ni bokanya ce kuma ba na tsoron kowa sai Ubangiji. Idan ban shiga hakkinka ba, baba so ka shiga nawa.
“Yan sandan Najeriya sun shiga gonata kuma sai sun gane kurensu. Yanzu haka ina ofishin ‘yan sanda. Ni da bokaye irina mun daura dammarar yakarsu.
“Kila kun ji labarin yadda aka kama Ajafunke. Tabbas, kafin in dawo rafi, ‘yan sanda sun kama min makada na ba tare da sun yi musu komai ba.
“Na je da karfin ikona na kwato su. Ba su isa su rike min mutane na ba. Saboda nasan yadda zan bullo musu.
“Ban zo da wasa ba, ina da layu da sauran ababen tsafi da na tabbatar su na aiki. Babu wanda a isa ya ci mutuncin Ajefunke Osiyemi.
“Ko gwamnati bata isa ta ci mutuncina ba. Duk wanda yayi kuskuren hakan zai gabe kurensa. Ni Ajefunke nace hakan.”
Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar ‘yan sanda, Musiliu Smith yayi murabus
Babbar kwamishina ta biyu a hukumar ta PSC, babbar Alkali a kotun koli, Clara Ogunbiyi, wacce ke wakiltar bangaren shari’a ita ce ta karbi rikon kwaryar shugabar hukumar.
Lokacin da jaridar Vanguard ta tuntubi Kakakin Hukumar, Ikechukwu Ani kan ci gaban, ya tabbatar da murabus din amma ya bayyana cewa za a fitar da sanarwar a hukumance daga hukumar da ke bayar da cikakkun bayanai a Gobe Alhamis.
A baya an sami rahoton cewa an samu rashin jituwa tsakanin Sufeto Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman, da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda kan daukar ‘yan sanda aiki a wannan shekara ta 2022 wanda za a dauki kimanin ‘yan sanda 10,000.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com