27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Ƴan ta’adda sun halaka babban ɗa ga wani ɗan majalisa a jihar Bauchi

LabaraiƳan ta'adda sun halaka babban ɗa ga wani ɗan majalisa a jihar Bauchi

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun halaka babban ɗa ga ɗan majalisar dake wakiltar mazaɓar Dass, Baba Ali, a majalisar dokokin jihar Bauchi.

Abdul Burra, kakakin shugaban majalisar Abubakar Suleiman, wanda ya gayawa wakilin jaridar The Punch yadda zaman majalisar ya kaya a ranar Talata, yace ɗan majalisar dake wakiltar mazaɓar Burra, Ado Wakili, shine ya bayyana hakan a zauren majalisar.

A cewar sa, ɗan majalisar wanda yayi wa sauran mambobin majalisar ta’aziyyar rasuwar ɗan abokin aikin su, ya lamarin a matsayin abin ban takaici.

Shugaban majalisar ya sanar cewa ƴan majalisar za su je ta’aziyya ga iyalan mamacin bayan sun kammala zaman su.

Yadda aka halaka babban ɗa ga ɗan majalisar

Burra yace Baballe Dambam, ɗan majalisa mai wakiltar Dambam/Zagaya/Jalam, ya bayyana cewa wasu mutane waɗanda ba a san ko su wanene ba suka sace mamacin inda suja tsare shi na tsawon kwanaki sannan daga ƙarshe suka halaka shi.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro da takaici, inda ya ƙara da cewa tuni har an yi jana’izar mamacin.

Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin

Kakakin hukumar ƴan sandan jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakil, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga ƴan jarida, ya kuma ce ƴan bindigan sun sace mata biyu na mamacin da kuma wani yaro ɗan shekara ɗaya.

An sako su daga bayan sun kwashe kwanaki a tsare.

Ƴan bindiga sun farmaki tawagar ɗan takarar gwamnan APC a Kaduna, sun sace jiga-jigan jam’iyyar

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun farmaki tawagar ɗan takarar gwamnan APC a Kaɗuna, sun yi awon gaba da wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Ƴan bindiga sun sace wasu ƙusoshin jam’iyyar APC a jihar Kaduna a wani harin da ya auku akan hanyar Kaduna-Kachia a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa harin ya auku ne a wani waje da ake kira Tashar Icce wanda yake kusa da ƙauyen Kujama a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.

Tawagar ta su tana kan hanyar dawowa daga Kafanchan bayan kammala wani taron siyasa da shugabannin Kiristoci a ranar Alhamis.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe