31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Kotu tayi watsi da Ahmed Lawan, ta bayyana Machina a matsayin sahihin ɗan takarar APC

LabaraiKotu tayi watsi da Ahmed Lawan, ta bayyana Machina a matsayin sahihin ɗan takarar APC

Wata babbar kotun tarayya mai zaman ta a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ta bayyana Bashir Sheriff Machina a matsayin sahihin ɗan takarar sanatan APC na Yobe ta Arewa a zaɓen ƴan majalisu mai zuwa na shekarar 2023.

Kotun ta kuma umurci hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta wallafa sunan sa kamar yadda ya dace. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Mai shari’a Fadima Aminu, itace ta bayar da wannan umurnin a ranar Laraba, a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

An zaɓi Machina bisa ƙa’ida

Mai shari’ar ta tabbatar cewa an zaɓi Machina a matsayin ɗan takarar sanatan APC na Yobe ta Arewa a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a ranar 28 ga watan Mayun 2022.

Lawan ya faɗi zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, inda yasha kashi a hannun tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Sai dai, yayi ƙoƙarin samun tikitin takarar sanatan Yobe ta Arewa wanda Machina ya lashe amma bai samu nasara ba, inda Machina yayi biris ya ƙi yarda ya ba shi tikitin.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya yiwa Machina barazana

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya gargaɗi Machina cewa idan har bai bayar da tikitin ga Ahmed Lawan ba zai iya fuskanci hukunci mai tsauri.

Adamu yayi iƙirarin cewa jam’iyya na gaba da kowa sannan tana da damar yanke hukuncin wanda zai samu tikitin ta a kowane zaɓe.

A cikin jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa da na ƴan majalisu da INEC ta fitar satin da ya gabata, ba a saka sunan kowane ɗan takara ba a Yobe Arewa, ba a rubuta komai ba a wurin.

Mun jinjinawa Osinbajo da Boss Mustapha bisa watsi da tikitin Muslim-Muslim na APC -Daniel Bwala

A wani labarin na daban kuma, Daniel Bwala ya yabawa Osinbajo da Boss Mustapha bisa watsi da tikitin Muslim-Muslim na APC

Daniel Bwala, kakakin yaƙin neman takarar shugaban ƙasa na Atiku Abubakar, yace ya jinjinawa mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, bisa watsi da suka yi da tikitin Muslim-Muslim na jam’iyyar All Progressives Council (APC).

Maganar ta Daniel Bwala na zuwa ne bayan ba a saka sunayen Osinbajo da Boss Mustapha a cikin jerin sunayen mutanen da zasu jagoranci yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe