
Wata babbar kotun tarayya da ke Sokoto a ranar Larabar da ta gabata ta bayar da umarnin a tsare wani darakta a hukumar kula da kayayyaki ta jihar Sokoto, Hassan Bello, a gidan gyaran hali bisa zargin badakalar naira miliyan 1.3 na aiki.
Mai shari’a Ahmad Mahmud shi ne, ya bayar da umarnin a tsare Hassan Bello bisa kamasa da laifin
Mista Mahmud ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 4 ga watan Oktoba, domin sauraren karar neman belin da kuma shari’a.
Hannafi Sa’ad ma’aikaci a Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ya shaida wa kotu cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne tun a watan Agustan shekarar 2021.
Mista Bello, wanda shi ne Daraktan Gudanarwa na hukumar an ce ya karbi kudaden ne daga hannun Aliyu Adamu-Tsaki, Yusuf Abubakar da Yahaya Salihu a gaban Dahiru Muhammad a Sokoto.
EFCC ta yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya gabatar musu da takardun aiki na karya wanda daga baya aka gano na karya ne kuma babu su.
NAN
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com