37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

“Ina jin ƙamshin mutuwa wata bakwai kawai suka rage min” Cewar budurwa cikin kuka

Labarai"Ina jin ƙamshin mutuwa wata bakwai kawai suka rage min" Cewar budurwa cikin kuka

Bidiyon wata budurwa wacce tayi iƙirarin cewa wata bakwai kawai ya rage mata a duniya ya sosa zuƙatan mutane a yanar gizo.

Budurwar mai suna Malkai ta garzaya manhajar TikTok cikin kuka inda ta koka kan yadda ta gaji sannan ta rasa ƙwarin guiwar cigaba da rayuwa.

Ta bayyana cewa tana iyakar bakin ƙoƙarin ta amma abubuwa sun ƙi tafiya daidai. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Ta bayyana halin da take ciki

A kalamanta:

Ina da saura wata bakwai kawai, amma bani da ƙwarin guiwar cigaba da rayuwa, na gaji, ba zan iya cigaba da ƙoƙartawa ba.

Ina ƙoƙartawa amma komai yaƙi tafiya daidai, wannan shine kawai. Ba zan iya cigaba da daɗewa anan ba.

Kalli bidiyon a nan

Sai dai ba a san haƙiƙanin abinda take ƙoƙarin nunawa ba ta hanyar cewa saura wata bakwai kawai ya rage mata ba.

Mutane da dama sun tausaya mata

Zam Nabayaza ya rubuta:

Idan kin ji ba zaki iya jurewa ba, ki zauna kawai ko ki fita daga cikin gida ki tafi ofishin ƴan sanda, idan kika je za su yi miki tambayoyi, kada ki basu amsa ki ce musu kawai keny

Nze phoebe ❤ ta rubuta:

Ki gudu ba zan iya cewa ina jin raɗaɗin abinda kike ji saboda ke kaɗai ce kika san halin da kike ciki, ina jin takaici duk lokacin da na ƴan’uwan ƴan Afrika na shan wahalana gidajen su.

nakabonge Victoria ta rubuta:

Ƴar’uwa daidai ne kiji kin gaji amma ba daidai bane guiwoyin ki su sare. Kada ki taɓa gazawa har sai yaƙin ya ƙare, ni ina da sauran shekara ɗaya kawai.

Budurwa ta kunshi takaici bayan raka kawarta da saurayi wurin cin abinci, ya ki siya mata komai

A wani labari na daban kuma, wata budurwa ta ƙunshi takaici baya ta raka ƙawarta da saurayinta wurin cin abinci bai siya mata komai ba.

Samari da dama sun yaba wa wani matashi wanda ya dauki wani tsatstsauran mataki akan kawar budurwarsa bayan ta raka budurwar tare da shi wurin cin abinci, Legit.ng ta ruwaito.

Mutumin ya ki siya wa kawar komai a bidiyon kuma ya nuna halin ko in kula duk da dai bidiyon ya nuna yadda kawar ta shiga damuwa. Nan da nan aka dinga yada bidiyon wanda aka ganshi da budurwarsa su na morar abincinsu yayin da ita kuma kawarta ke zaune babu komai a gabanta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe