37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Tsohon kyaftin din Super Eagles Mikel Obi ya yi ritaya daga buga kwallo

LabaraiTsohon kyaftin din Super Eagles Mikel Obi ya yi ritaya daga buga kwallo
Concise News.jpeg

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Mikel Obi ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo a hukumance.

Dan wasan mai shekaru 35 ya bayyana hakan ne a shafin sa na Instagram a ranar Talata.

Mikel ya gode wa duk wandanda suka bada gudummawa ta wata hanya ko wata nasara da ya samu a harkar kwallon kafa.

Tsohon kyaftin din na Super Eagles ya kassnce daya daga cikin fitattun taurarin kwallon kafa na Afirka, inda ya lashe kyautar azurfa da dama a kungiyoyi da kuma kasarsa.

A kulob din Chelsea inda ya shafe mafi aikinsa a can, Mikel ya taimaka wa Blues a gasar cin kofin zakarun Turai na farko a 2012.

A lokacin da ya ke Landan, dan wasan mai lambar tsakiya ya daukaka duk wata babbar karramawa, wanda ya hada da kofunan Premier guda biyu, gasar zakarun Turai da kuma Gasar Turai, Kofin FA, da Gasar Carling da sauransu.

Ya buga wasanni 372 a cikin kulob din Chelsea.

Mikel ya kuma taba taka leda a kasashen China, Turkiyya da Kuwait kafin ritayar sa.

Ga cikakken bayanin Mikel kan ritayarsa:

Masu iya magana na cewa “dukkan abinda ya yi farko dole yayi karshe”, a aikina na wasan ƙwallon ƙafa, wannan ranar ita ce yau, “cewar sakon.
‘Nasara bata faruwa sai da goyon bayan dangi Ba tare da goyon bayan manajoji, kocina, abokan wasa da kuma mafi mahimmancin magoya bayana masu aminci da ban kawo zuwa yanzu ba.

‘Ba bankwana nakeyi ba ,wannan farkon wata tafiya ce, wani babi na rayuwata. Ina sa ran abin da zai faru nan gaba kuma ina fatan za ku kasance tare da ni Na gode.’

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe