37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Magidanci na son amsar hotunan tsiraicin tsohuwar matarsa don ya dinga tunawa da ita

LabaraiMagidanci na son amsar hotunan tsiraicin tsohuwar matarsa don ya dinga tunawa da ita

Wata mata daga Utah, can Amurka ta bayyana yadda wani Alkali ya umarceta da ta bai wa tsohon mijinta albam din hotunan tsiraicinta a matsayin daya daga cikin abubuwan da ya bukata don ya sake ta, LIB ta ruwaito.

Sai dai a cewar Lindsay Marsh, ta taba yin hotunan ne a farkon aurensu inda ta hada masa da kalamai masu dadi na soyayya a albam din. A watan Afirilun 2021 bayan kwashe shekaru 25 da aurensu, tsohon mijinnata ya bukaci ta bar masa albam din hotunan don ya dinga tunawa da ita.

A cewarta, kawai wannan shirin tozartata da wulakanta ta aka yi. Ta bayyana cewa ya labarta yadda su ka yi ne ga mutane don su ji su hankalta don gudun fadawa makamancin yanayin da take ciki a halin yanzu.

A cewar Marsh, ta yi mamaki akan yadda mijin nata ya nemi wannan albam din yanzu da suke shirin rabuwa. Sai dai Alkalin, Micheal Edwards, mai zama a 2nd district court, ya bi bayan tsohon mijin nata.

Alkalin ya bukaci ta mayarwa asalin wanda ya dauketa hoton don ya cire duk inda jikinta ya fito a albam din. Bayan Marsh ta je wurin mai hoton, ya ba zai iya yin hakan ba. Ganin haka Alkalin ya bukaci ta bai wa wani mai hoton na daban don ya cireta a hotunan.

Kamar yadda Alkalin ya bukata, duk wanda zai gyara hotunan zai ga inda ta bayyana da kamfai da rigar mama ko kuma wanda babu komai a jikinta sannan ya cireta a ciki.

Ta ce alkalin ya bukaci ta bayar da hotunan tsiraicinta ga wani na daban a matsayin mai yin gyara a hotunan ba tare da ya duba illar hakan ba. Ta ce ta kara kiran alkalin don ta kara ji ko bata fahimci hukuncinsa bane don ya jaddada mata bayani.

Matar aure taci bakin duka a hannun budurwar mijinta bayan ta gaura mata mari

Ganau ya bayyana yadda budurwar mijin wata mata ta yi mata bakin duka inda ta bar ta warwas a kasa a titin Ibadan, LIB ta ruwaito. Wata matar aure ta tunkuri budurwar mijinta a Ibadan, sai dai abin bai kaya dakyau ba.

An samu bayanai akan yadda matar auren ke tuka wata mota inda ta hango wata budurwa cikin motar mijinta daidai kwanar Iyaganku-Aleshinloye, hakan yasa ta zargi budurwar mijinta ce.

Nan ta dakata ta fito daga cikin motarta inda ta gaura wa budurwar mari a fuska. Ganin hakan ne yasa budurwar ta fito daga motar ta nana matar auren da kasa tare da ci gaba da lakadarta kamar yadda ganau din ya shaida.

Nan da nan mutane su ka taru bayan ganin matar auren kwance a kasa warwas. A cewarsa, yayin da yake bayar da labari ya ga yadda ‘yan sanda su ka tunkari inda matar ta baje a kasa yayin da budurwar ta gama bazgarta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe