37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Budurwa ta kunshi takaici bayan raka kawarta da saurayi wurin cin abinci, ya ki siya mata komai

LabaraiBudurwa ta kunshi takaici bayan raka kawarta da saurayi wurin cin abinci, ya ki siya mata komai

Samari da dama sun yaba wa wani matashi wanda ya dauki wani tsatstsauran mataki akan kawar budurwarsa bayan ta raka budurwar tare da shi wurin cin abinci, Legit.ng ta ruwaito.

Mutumin ya ki siya wa kawar komai a bidiyon kuma ya nuna halin ko in kula duk da dai bidiyon ya nuna yadda kawar ta shiga damuwa. Nan da nan aka dinga yada bidiyon wanda aka ganshi da budurwarsa su na morar abincinsu yayin da ita kuma kawarta ke zaune babu komai a gabanta. Wanda ya wallafa bidiyon a TikTok har zolayar kawar yayi wacce aka ganta zaune cike da damuwa. Har yana cewa sai da aka ja kunnen kawarta akan kada ta kuskura ta je da kowa. A bidiyon, an lura da yadda matashin ke morar abincinsa shi da budurwarsa yayin da ta gefensu ke zaune cike da damuwa. Mutane da dama sun yi ta caccakar budurwar akan yadda ta bari har saurayinta ta tozarta mata kawa, yayin da maza su ka dinga yaba wa saurayin akan share kawar budurwarsa da yayi.

Saurayi ya nemi yafiya wurin budurwarsa da N10m, hotunan sun ɗauki hankula

Wani matashin saurayii ya ja hankulan masu amfani da yanar gizo da hanyar sa ta musamman ta neman yafiya a wurin budurwar sa.

Matashin saurayin yayi wani abin ban mamaki wanda ya ɗauki hankulan mutane kan yadda ya nemi yafiya a wurin budurwar sa bayan ya ɓata mata rai.

Saurayin ya bata makuɗan kuɗaɗe don neman yafiyarta

Matashin saurayin dai ya bayar da tsabar kuɗi har naira miliyan goma, ƴar bebin roba da wasu kyaututtukan na musamman. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

A wasu hotuna da suka karaɗe yanar gizo, kyakkyawar budurwar ta riƙe wani allon rubutu da saurayin nata ya bata. A jikin allon rubutun an rubuta ‘yi hakuri’

Lamarin ya ɗauki hankula sosai, inda mutane da dama suka yi ta magana akai

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su kan lamarin, masu amfani da yanar gizo sun nuna jindaɗin su kan abinda matashin yayi. Yayin da wasu ƴanmatan kuma suka ji dama ace sune abin ya faru da su, wasu kuma sun nuna matuƙar kaduwar su akan lamarin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe