32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Jami’an DSS sun cafke wani soja mai safarar makamai ga ƴan ta’adda a Abuja

LabaraiJami'an DSS sun cafke wani soja mai safarar makamai ga ƴan ta'adda a Abuja

Jami’an hukumar farin kaya ta DSS sun cafke wani soja a Abuja bisa zargin bada haya da siyar da bindigu ga masu garkuwa da mutane.

Sojan yana aiki a sansanin Muhammadu Buhari a Tungan-Maje a birnin tarayya Abuja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an cafke sojan ne satin daya gabata a kusa da wurin shaƙatawa na Dankogi a Zuba tare da haɗin guiwar mambobin ƴan sakai na yankin.

Jami’an DSS sun yi haɗin guiwa da ƴan sakai wurin kama shi

Wani majiya a cikin ƴan sakan ya bayyana cewa jami’an DSS daga ofishin Gwagwalada sun nemi taimakon ƴan sakai na Zuba domin cafke wanda ake zargin bisa zarge-zargen safarar makamai da akai masa a baya.

An fahimci cewa wanda ake zargin, a cinikin farko ya bada hayar bindiga kan kuɗi N300,000.

Sannan a karo na biyu sun tuntuɓe shi domin wani cinikin inda ya buƙaci su bashi N200,000, kuma sun biya amma bai kawo musu bindigar ba.

Yadda aka shirya kama sojan

Majiyar ta bayyana cewa lokacin da ƴan ta’addan waɗanda suke tsare a hannun DSS suka zargi sojan, an yi wani kyakkyawan shiri domin kama shi.

Sai suka ƙara tuntuɓar sa domin ya samar musu da AK-47 wacce za su siya akan kuɗi miliyan uku.

Mun je wurin da aka shirya a ranar da za a kawo bindigar a nan Zuba, sannan muka laɓe. Ya zo wurin a cikin motar sa domin bada bindigar, a sannan ne muka fito muka kama shi da bindigar an nannade ta.

Majiyar ta kuma bayyana cewa an samu bindiga ƙirar AK-47 da gidan harsashi cike da harsasai guda talatin a cikin motar sa.

Mun tafi da shi zuwa ofishin mu inda muka rattaɓa hannu kan wasu takardu da jami’an DSS sannan muka miƙa shi a hannun su.

Ƴan sanda sun cafke masu safarar makamai da kayan sojoji ga ƴan bindiga a Zamfara

Hukumar ƴan sandan jihar Zamfara ta cafke masu bada bayanai da safarar makamai ga ƴan bindiga a jihar.

Kakakin hukumar, Mohammed Shehu, shine ya sanar da hakan yayin zantawa da ƴan jarida a ranar Asabar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe