32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Matar aure taci bakin duka a hannun budurwar mijinta bayan ta gaura mata mari

LabaraiMatar aure taci bakin duka a hannun budurwar mijinta bayan ta gaura mata mari

Ganau ya bayyana yadda budurwar mijin wata mata ta yi mata bakin duka inda ta bar ta warwas a kasa a titin Ibadan, LIB ta ruwaito. Wata matar aure ta tunkuri budurwar mijinta a Ibadan, sai dai abin bai kaya dakyau ba.

An samu bayanai akan yadda matar auren ke tuka wata mota inda ta hango wata budurwa cikin motar mijinta daidai kwanar Iyaganku-Aleshinloye, hakan yasa ta zargi budurwar mijinta ce.

Nan ta dakata ta fito daga cikin motarta inda ta gaura wa budurwar mari a fuska. Ganin hakan ne yasa budurwar ta fito daga motar ta nana matar auren da kasa tare da ci gaba da lakadarta kamar yadda ganau din ya shaida.

Nan da nan mutane su ka taru bayan ganin matar auren kwance a kasa warwas. A cewarsa, yayin da yake bayar da labari ya ga yadda ‘yan sanda su ka tunkari inda matar ta baje a kasa yayin da budurwar ta gama bazgarta.

Ga bayani dalla-dalla:

A rabamu, mijina ba ya tabuka min komai a shimfidar aure, Matar aure ga kotu

Wata ‘yar kasuwa, Monica Gambo, a ranar Juma’a ta maka mijinta, Yakubu Gambo gaban kotun Nyanya da ke Abuja akan kin bata hakkinta na aureNigerian Pulse ta ruwaito.

Ya bayyana yadda ya tare a wurin karuwai yana yin masha’arsa yadda yaga dama. Ta kara da cewa:

“Yana hana ni hakkin aurena don haka ba zan iya ci gaba da zama da shi ba.”

Ta ci gaba da shaidawa kotu yadda mijinta yayi yunkurin halaka ta don kwashe dukiyarta.

Ta bukaci kotu ta raba aurensu ta kuma umarci mijinta da ya kwashe komatsansa ya bar mata gidanta.

Mijin nata, Yakubu Gambo, wanda tela ne ya musanta duk zargin da take yi masa. Daga nan ne Alkalin kotun, Shettima Mohammed ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Satumba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe