29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

An gano wata jami’a da ke biyan dalibai albashi kuma tana karantarwa a kyauta

IlimiAn gano wata jami'a da ke biyan dalibai albashi kuma tana karantarwa a kyauta

An gano wata jami’a da ke kasar waje wacce ke biyan dalibai albashi kuma ana karatu kyauta. Wata ma’abociya amfani da suna @qsgreenland ta bayyana wani bidiyon wata jami’a da ke Greenland a arewacin Amurka inda ake karatu kyauta, Legit.ng ta ruwaito.

A cewarta, ana biyan dalibai albashi ne a ko wanne wata don suyi karatu. Yayin tattaunawar da tayi da wani dalibi, Pele, wanda ke karatun walda na shekaru 4 ta bayyana yadda ta kaya musu.

Wannan bidiyon ya ja hankalin talakawan Najeriya inda su ke ganin ya dace su lallaba ganin yadda yajin aiki ya taso su gaba aka kasa kammala karatu. A cewarta, akwai yuwuwar karatu bai gama ratsa ‘yan kauyen bane.

Ga tsokacin ‘yan Najeriya karkashin bidiyon:

Bolaji yace:

“Ina da ra’ayin shiga makarantar daga Najeriya, ya zan yi?”

Fkay4real tace:

Ya za ayi in shilla? Daga Najeriya.

Sijia tace:

Ina son zuwa Greenland yanzu.”

Emily yace:

Ina Newfoundland, Canada, muna kusa da Greenland! Har na siya tikitin zuwa Greenland zan kai ziyara!

Tiaquicyl tace:

Shin su na amincewa da daliban kasashen waje?

Jedu’sTech yace:

Ya zan yi a dauki nauyin karatuna daga Najeriya?”

Riched360 yace:

“Daga Jamaica nake. Zan so sanin karin bayani cikin gaggawa.”

Bayan fadi darasinsa, dalibai 11 sun daure malamin lissafi jikin bishiya, sun lakada masa dukan tsiya

Rundunar ‘yan sanda ta ruwaito yadda dalibai 11 su ka taru wurin daure malamin lissafinsu jikin bishiya tare da zane masa jikinsaNigerian Pulse ta ruwaito.

Sai da su ka ja shi zuwa harabar marakantar da sunan za su tattauna da shi dangane da wata jarabawar da ya basu har su ka fadi.

Daga nan ne su ka kama malamin, Suman Kumar, bayan ya bayyana musu makin da su ka ci a shafin yanar gizon makarantar, Soneram Chaure, sannan su ka daure shi jikin bishiyar tare da zane shi.

Bidiyoyi da hotunan yadda lamarin ya auku sun bazu a shafukan sada zumunta inda kowa yaga yadda aka zane mutumin.

Kamar yadda odditycentral.com ta ruwaito, bincike ya bayyana yadda daliban su ke a fusace inda daya daga cikinsu ya nuna dukan da malamin yayi masa bayan ya fadi darasin har da bandeji a kansa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe