32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Bayan watanni 2 da aurensu, ango ya banka wa kansa wuta saboda amarya na fushi da shi

LabaraiBayan watanni 2 da aurensu, ango ya banka wa kansa wuta saboda amarya na fushi da shi

Bayan watanni biyu da wani dan shekara 30 yayi aure, matarsa tana yawan zagi da kushe shi. Afolabi, mazaunin yankin Iree ne da ke Jihar Osun, an samu nasarar ceto shi bayan ya banka wa kansa wuta, Nigerian Pulse ta ruwaito.

An tattaro bayanai akan yadda mutane su ka kai masa dauki bayan jin ya fara rusa kuka. Ya bayyana cewa ya yi aure ne a watan Yulin 2022, kuma matarsa tana yawan azabtar da shi, hakan ne ya tunzura shi ya yanke shawarar halaka kansa.

Afolabi ya yi bayanin ne a gadon asibiti inda yace bakar azabar da amarya ke gallaza masa ne ya sa ya dauki matakin. A cewarsa, tun da su ka yi aure ta fara azabtar da shi.

Kamar yadda ya bayyana:

Na yanke shawarar kawo karshen komai ne a ranar Juma’a shiyasa na je har gidan mai na siyo man fetur. Na nufi dajin kusa da makarantar Baptist da ke Iree inda na banka wa kaina wuta.

Na yi tunanin azabar da nake sha ne yasa na yanke shawarar halaka kaina. Bakin talauci da azabar da matata ke min yasa na dauki wannan matakin. Na aure ta ne a watan Yulin wannan shekarar.

Jama’a ne su ka ji ni ina ihu yayin kona jikina shi ne su ka yi gaggawar ceto ni su ka kai ni asibiti.”

Matar Afolabi, Ifedolapo ta ce bata san dalilin da yasa zai halaka kansa ba. Amma tana zaton saboda har yanzu bata samu juna biyu bane ya yanke shawarar halaka kansa.

Yadda ango ya fasa auren amarya bayan ta ki sanar da shi wanda ya siya mata IPhone 13 Pro Max

Wani matashi ya fasa auren budurwarsa bayan ta ki fada masa wanda ya siya mata waya kirar IPhone 13 Pro Max kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Dama an sa ranar aurensu ne kuma su na ta shirye-shirye, kwastam rannan tazo gida da waya IPhone 13 Pro Max.

Nan da nan masoyin nata ya bukaci sanin wanda ya siya mata wayar inda ta sanar da shi cewa dan uwanta ne.

Da ya ci gaba da bincike inda ya nemi sanin sunansa sai ta ki fadi wanda hakan yasa matashin ya fusata ya fasa auren.

An samu bayanin ne bayan abokin ango mai amfani da suna @Rita_Amy ya labarta yadda lamarin ya auku.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe