32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Allahu Akbar: Ana tsaka da musabakar Al’Qur’ani, Malama Taslimah ta kwanta dama tana Tilawa

IlimiAllahu Akbar: Ana tsaka da musabakar Al’Qur’ani, Malama Taslimah ta kwanta dama tana Tilawa

A wata musabakar Al’Qur’ani mai girma da ake yi a masallacin Albarkah KH Abdallah Syafie, da ke Kampung Melayu a yammacin Jakarta a kasar Indonesia, Malama Taslimah ta rasu a ranar 15 ga watan Satumban 202, The Islamic Information ta ruwaito.

A lokacin tana tsaka da tilawar aya ta 4 zuwa ta 6 a cikin suratul Baqarah. Nan da nan aka ji sautin muryarta ya karye bayan ta shiga aya ta 6.

Taron mata sun yi gaggawar zuwa kai mata dauki inda suka rike ta kafin ta karasa faduwa.

A ranar Alhamis da safe, Malama Ita Rasyid AS, daya daga cikin mambobin kungiyar Syafi’iyah Ummahat Ta’lim ta bayyana yadda asali Malama Taslimah daga Tanjung Barat, da ke kudancin Jakarta take.

Yayin taron taklim, Malama Taslimah ta kasa ci gaba da magana saboda halin da take ciki.

Wata mai amfani da suna @agfabetawie ta bayar da wannan bayanin inda tace a ranar Alhamis, 15 ga watan Satumban 2022 da misalin karfe 7:45 Malama Taslimah rasu tana karatun Qur’ani a masallaci.

Ƴar baiwa: Yadda wata ƙaramar yarinya ta haddace sannan ta rubuta Al-Qur’ani a Katsina

Wata ƙaramar yarinya mai shekara 13 a duniya, Zuwaira Ahmed, a ƙauyen Kagara na ƙaramar hukumar Kafur a jihar Katsina, ta haddace sannan ta rubuta Al-Qur’ani mai girma hizifi sittin da hannu.

Da yake magana a wurin walimar da aka shirya domin ƙarrama yarinyar a ranar Asabar, hakimin Mahuta, Alhaji Bello Abdulkadir, ya nuna farin cikin sa akan wannan gagarumin cigaban da aka samu.

Yayi bayanin cewa wannan gagarumar nasara ce da aka samu a ƙauyen, da jihar gabaɗaya musamman a fannin ilmin addinin musulunci. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Abdulkadir ya kuma yabawa iyayen yara na yankin, malamai da sauran jagororin al’umma bisa tabbatar da cewa yaran su sun taso cikin tarbiyya mai inganci inda ya nemi da su cigaba akan wannan turbar.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Kafur, Alhaji Garba Abdullahi-Kanya, ya yaba sosai da abinda yarinyar tayi inda ya bada tabbacin goyon bayan karatun ta tun daga matakin sakandire har zuwa na gaba da sakandire.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe