32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Yadda gini ya rufta da karuwa da kwastoma yayin da suke gwada bajimtarsu a kan gado

LabaraiYadda gini ya rufta da karuwa da kwastoma yayin da suke gwada bajimtarsu a kan gado

Jami’an bayar da taimakon gaggawa sun bayyana labarin yadda gini ya rufta a Jihar Legas ranar Juma’a 23 ga watan Satumban 2023, LIB ta ruwaito.

Kamar yadda rahoton ya nuna, ginin gida mai lamba ta 2/4 kan titin Sonuga da ke Palm Avenue a Mushin, ya rufta a ranar Juma’a inda yayi sanadiyyar mutuwar mutane hudu.

Yayin tattauna da Daily Trust, jami’an bayar da taimakon gaggawa sun bayyana yadda cikin mutane hudun akwai mutane biyu wadanda da mace da namiji ne. Su na tsaka da lalata lamarin ya auku.

A cewar jami’in:

“Su na tsirara lokacin da aka tsinci gawarwakinsu.

Wani jami’in wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce.

Mun yi mamakin ganin wannan al’amari. Mutane biyun da muka tsinta gaskiya su na tsaka da lalata ne. Namijin yana kan karuwar ne ginin ya rufta musu. Anan ne dukansu su ka mutu.”

Wani jami’i daban cewa yayi ginin dama matattara mata ne wadanda kowa ya san karuwai ne. A cewarsa:

“Wurin dama gidan mata karuwai ne. Saboda wadanda mu ka tsinta daga baya mace ne da namijin kwastomanta. Su na tsaka da sheke ayarsu aka tsinci gawarsu.”

Dayar majiyar ta ce:

“Mun yi wa abokan harkarsu, wadanda su ma karuwai ne inda su ka samar da mu komai dangane da su har da ‘yan uwansu don su san halin da ake ciki.”

Ana gama birne mai gidan karuwai, wata karuwa ta gayyaci kwastoma don lalata kan kabarinsa

‘Yan sanda a Mutare su na neman masu rakon gawar da su ka yi tsirara kafin fara lalata akan wani kabari da ke makabartar Dangamvura da tsakar rana, Hourlyhits.com ta ruwaito.

Lamarin mai ban mamaki ya auku ne a ranar Alhamis din da ta gabata yayin birniyar wani mai gidan karuwai a Mutare cikin kasar Zimbabwe.

Mummunan al’amarin ya auku ne bayan kammala birne gawar marigayi Maroni Mazvita Karinda.

Tuni jama’a su ka ji labarin wanda aka dinga yadawa a kafafen sada daban-daban bayan ‘yan rakon gawar sun yi bidiyoyi guda biyu.

Tatenda ce ta nemi wani namiji ya zo yayi lalata da ita

Bidiyon ya fara ne bayan wata mata, fitacciyar karuwa wacce aka fi sani da Tatenda ko Mai Keisha, ta fara yin tsirara tana neman wani namiji ya zo yayi lalata da ita.

Hakan ya auku ne gaban duk masu rakon gawar wadanda ba su dade da birne Karinda ba, mai gidan karuwan Sakubva, mai shekaru 45.

Nan da nan wani ya amsa goton gayyatar kuma an fahimci cewa yana yawani zama ne a kusa da titin Sakubva.

Masu rakon gawar sun hada baki su na cewa “bvisa, bvisa, bvisa, bvisa” (ma’ana tube kayanka), inda mutumin ya hau cire kaya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe