32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Matashin Bakanon da yayi wuff da dattijuwar Baturiya ya ce mahassada sun tasu su gaba

LabaraiMatashin Bakanon da yayi wuff da dattijuwar Baturiya ya ce mahassada sun tasu su gaba

Wani dan Jihar Kano mai shekaru 24 wanda ya auri baturiya mai shekaru 48 ya bayyana yadda mahassada su ka tasa shi gaba inda su ke fatan aurensa ya mutu, LIB ta ruwaito.

A cewar Suleiman Isah, wanda ya auri dattijuwar baturiyar nan, Janine Sanchez Reimann, akwai mutane da dama da ke jiran jin labarin aurensu ya lalace.

Idan ba a manta ba, sun yi aure ne a ranar 13 ga watan Disamban 2020, a wuraren Gasau Panshekara da ke cikin Jihar Kano bayan haduwarsu a Instagram.

A cewar Isah, akwai mutane da dama da ke ce masa ya tsero ya dawo Kano da zarar auren ya lalace.

A cewarsa:

Ina mamakin yadda mutane ke ce min, da zarar batirina ya yi kasa, wajibi ne in dawo Kano in zauna,” kamar yadda ya wallafa a ranar Lahadi, 25 ga watan Satumba.

Shehu Sani ya yi masa tsokaci inda yace:

Hassada kenan.” Inda shi kuma ya amsa shi da cewa, “Wallahi kuwa Ranka shi dade, ba su da ilimi akan harkar komawa Amurka.

Babbo yace, “Ka toshe su mana, makiya ne tun daga zuciyarsu.”

Ameer Lukman Haruna yace, “Ba su san zoben har abada bane ba na aure kawai ba.” Inda yace: “Hakane dan uwa, basu sani ba.”

Ina samun kai na cikin farin ciki a duk lokacin da nake tare da ke – Suleiman Isah ga matar shi Baturiya

Matashin nan dan Najeriya mai shekaru 24 dan asalin jihar Kano, Suleiman Isah, ya wallafa rubutu a kafar sada zumunta na yanar gizo a kokarin da yake na taya matarsa Janine Sanchez Reimann murnar cika shekaru 48 a duniya.

Da yake bayyana hakan a shafin sa na Facebook, cikin nuna farin ciki Suleiman Isah ya daura kyawawan hotunansu shi da matar tasa wanda a hoton kadai za a fahimci yanda suke matukar kaunar junansu.

Inda yake bayyana ma duniya cewar fa matar sa daban take da sauran mata, tayi musu zarra, ya kara da cewa yana matukar sonta, kuma yana alfaharin kasancewan su tare.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe