32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Yadda jariri ya mutu a hannun budurwa daga taya mamarshi rike shi a motar haya

LabaraiYadda jariri ya mutu a hannun budurwa daga taya mamarshi rike shi a motar haya

Wata budurwa ta ci dukan tsiya a hannun matasa bayan jariri ya kubuce a hannunta ya mutu a tashar mota kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Wata ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, @Shesamale ta ruwaito yadda budurwar ta taya matar rike jaririnta a motar haya bayan matar ta bukaci hakan.

Shasamale ta ce tana isa matar ta bukaci ta taya ta rike jaririn inda ta ki amincewa, hakan yasa matar ta je wurin wata wacce ta amince.

Ta ce yayin da suke kokarin shiga motar ne jaririn ya kubuce daga hannun budurwar ya fadi kuma take anan ya mutu. Nan da nan matar ta hau kururuwa tana cewa akwai abinda budurwar tayi wa jaririnta.

Nan da nan fusatattun matasa su ka taru su ka lakada wa budurwar duka wacce jaririn ya fadi a hannunta. Lamarin ya auku ne a wata tashar mota da ke Portharcourt.

Nan da nan mutane su ka dinga tsokaci karkashin wallafar.

Batman yace:

Maganar gaskiya idan har ka fita waje, ya kamata ka fita harkar mutane. Gara ka sanya abin jin sauti na kunne ka kuma dode idonka da gilashi, hakan yana kare ka daga abubuwa da dama.”

Kay Kayode yace:

Ni gaskiya bana amincewa da irin haka. Haka fa na taimaki wata mata na daura mata diyarta a cinya. Yarinyar ta jike min jiki da fitsari. Ko hakuri ba su ba ni ba. Kawai fita su ka yi su ka wuce. Babba da ni an jike min wando da fitsari. Abin akwai ban takaici.”

Agboola Starr tace:

Wannan ai hauka ne. Kila ma damfara ce. Daga nan za a bukaci ta biya makudan kudade. Kuma jaririn zai tashi bayan ta yi wasu abubuwan. Na taba jin labarin irin haka. Kila kuma ba haka bane. Na ji dadi da Ubangiji ya tsare ki.”

TherealBorme yace:

Na tuna wacce ke ce wa diyarta “zauna a cinyar kawu”.. Kawai janye kafata nayi yarinyar ta fadi.”

Budurwa ta siyar da jaririnta mai sati uku a duniya kan kuɗi ƴan kaɗan

Jami’an ƴan sanda a jihar Ogun sun cafke wata budurwa mai shekara 23, Mary Olatayo, bisa zargin siyar da jaririnta mai sati uku a duniya kan kuɗi N600,000

.

An dai cafke budurwar ne bayan da mahaifin jaririn ya shigar da ƙorafi a ofishin ƴan sanda na Mowe a ƙaramar hukumar Obafemi-Owode ta jihar Ogun.

Jaridar Daily Trust ta ambato kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.

Budurwar na soyayya da mahaifin jaririn

Mahaifin jaririn ya gayawa ƴan sanda cewa soyayya suke yi da budurwar sannan sai ta samu cikin sa.

A cewar sa, mahaifin jaririn yace ya kama mata gidan haya inda ta rayu har zuwa lokacin da ta haifi jaririn.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe