32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

An gwangwaje yaro mai aikin birkilanci yana kuka da sha tara ta arziƙi, an haɗa shi da mahaifiyar sa

LabaraiAn gwangwaje yaro mai aikin birkilanci yana kuka da sha tara ta arziƙi, an haɗa shi da mahaifiyar sa

Kamorudeen Yaron nan mai aikin birkilanci yana sharɓar kuka ya samu sha tara ta arziƙi bayan bayyanar bidiyon sa.

Bidiyon yaron wanda yake kuka yana aikin birkilanci ya sosa zuciyar mutane da dama, waɗanda suka tausayawa yaron bisa halin da yake ciki.

Yana aikin birkilanci don ya taimaki mahaifiyar sa

Ƙaramin yaron wanda maraya ne yana aikin na birkilanci ne domin ya taimaki mahaifiyar sa wacce take rayuwa a can wani ƙauye nesa da shi, kuma sau ɗaya kawai suke haɗuwa a shekara.

A wani bidiyon da Lukman Samsudeen mai amfani da @ayom_olanrewaju a TikTok ya sake sanyawa, ya nuna tagomashin da yaron ya samu wanda mutane suka haɗa masa.

An haɗa yaron da mahaifiyar sa

Lukman ya bayyana cewa sun sha matuƙar wahala kafin su gano inda mahaifiyar yaron take, domin tafiyar mai nisa ce ga kuma rashin kyawun hanya wanda hakan yasa har saida ɗaya daga cikin motocin su, ta lalace a hanya.

Ya kuma bayyana cewa an haɗawa yaron maƙudan kudaɗe da suka kai GHS650,000 (N27,332,500).

Daga ƙarshe dai sun samu sun haɗa yaron da mahaifiyar sa da ƴan’uwan baban sa, waɗanda duk suna rayuwa ne a ƙauye ɗaya.

Ƴan’uwan mahaifin yaron sun amince ya cigaba da karatun sa.

Kalli bidiyoyin a nan

Da kuma nan

“Mahaifiyata nake son taimako” Cewar yaro mai kuka yana aikin birkilanci

A wani labarin na daban da muka kawo muku a baya, wani yaro mai aikin birkilanci yana kuka ya bayyana dalilin da ya sanya yake wannan aikin ƙwadagon.

Bidiyon wani yaro mai aikin ƙwadago na birkilanci ya sosa zuciyar mutane da dama.

A cikin bidiyon an nuna yaron yana a wajen aikin birkilanci yana aiki yana kuka.

Bayan bidiyon sa na farko ya karaɗe yanar gizo, wanda ya wallafa bidiyon mai suna Lukman Samsudeen, ya bayyana wasu abubuwan ban tausayi dangane da yaron mai suna Kamarudeen. Jaridar Yen.com.gh ta rahoto.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe