37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Kada kuyi kuskuren zaɓar makasa a 2023 -Goodluck Jonathan ya gargaɗi ƴan Najeriya

LabaraiKada kuyi kuskuren zaɓar makasa a 2023 -Goodluck Jonathan ya gargaɗi ƴan Najeriya

A yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2023, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya shawarci ƴan Najeriya da kada suyi kuskuren zaɓar mutanen da ya kira a matsayin makasa su mulkesu.

Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa Jonathan ya bayar da wannan shawarin ne a ranar Lahadi 25 ga watan Satumba, a birnin Uyo a wajen bikin cika shekara 35 da ƙirƙirar jihar Akwa Ibom.

Goodluck Jonathan yace:

A 2023, kada ku kuskura ku zaɓi makasa.

Waɗanda za su ɗauki wuƙaƙe, bindigu da sauran makamai suje su kashe mutane saboda siyasa, sune maƙiyan al’umma. Idan kayi kisa domin zama shugaba, zaka cigaba da kisa domin zama a matsayin shugaba.

Goodluck Jonathan ya yabawa gwamna Udom Emmanuel

Tsohon shugaban ƙasar ya bayawa gwamnan jihar, Udom Emmanuel, bisa cigaban da ya kawo a jihar ta yankin Kudu maso Kudu

Yayi nuni da cewa lokacin da tsohon gwamnan jihar Goodswill ya bar kujerar mulki, akwai shakku kan rawar da Mr Emmanuel zai taka a jihar.

Duk da cewa gwamna Emmanuel ba gogaggen ɗan siyasa bane tun usuli, Jonathan yace Emmanuel yayi abin a zo a gani a shekara bakwai da yayi a kujerar mulki.

Yadda na kawo ƙarshen yajin aikin ASUU cikin kwana ɗaya -Goodluck Jonathan

A wani labarin na daban kuma, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana yadda ya kawp ƙarshen yajin aikin ASUU cikin kwana ɗaya.

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana yadda gwamnatin sa ta kawo ƙarshen yajin aikin da ASUU ta shafe wata huɗu tana yi cikin rana ɗaya.

Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, a wurin bikin cikar shekara 70 a duniya na Matthew Hassan Kukah, Bishop ɗin Katolika na Sokoto Diocese, wanda cibiyar Kukah ta shirya.

Yanzu haka malaman jami’a a Najeriya sun tsunduma yajin aiki tun watan Fabrairu bisa saɓanin dake tsakanin su da gwamnatin tarayya

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe