
Babban kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC, Dakta Ahmed Audi, ya yi alkawarin hukunta duk wani jami’in da aka samu da hannu a cikin satar mai a yankin Neja Delta.
Audi ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya ke jawabi a dandalin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.
Ya ce rundunar na gudanar da bincike kan rahotannin da ake zargin wasu ma’aikata da hadin gwiwar barayin mai a yankin Neja-Delta .
Audi ya kara da cewa hukumar NSCDC ta inganta tsarinta na ka’idojin aiki, tare da samar da isassun hanyoyin da za a bi wajen ladabtar da masu laifi.
“Mun amince da cewa za mu gudanar da sahihan bayanan sirri da bincike kan ayyukan jami’an mu da ake zargin suna da hannu wajen satar mai.
“Ina mai tabbatar wa ‘yan Najeriya da zarar mun kammala bincike, duk wanda aka samu da laifi za a hukunta shi.
Daukar Ma’aikata: Hukumar kula da gidajen gyaran Hali ta gargadi ‘yan Najeriya da suyi hattara da ‘yan damfara
Hukumar kula da gidajen gyaran Hali ta Najeriya, NCoS, ta gargadi masu neman aikin yi da su kula da kyau don gudun fadawa hannun ‘yan damfara, hukumar ta ce labarin cewar ta fara atisayen daukan ma’aikata karyane
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Umar Abubakar shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a yau Alhamis a garin Abuja.
Mista Abubakar ya ce Dolene su fito su gayawa jam’a don rage tasirin kokarin da ‘yan damfara ke yi na cuta ga masu neman aiki.
“Ma’aikatar ta samu labarin cewar an fitar da tallar karya na daukar ma’aikata.
“Wasu marasa kishin kasa ne ke yin wannan aikin dan su damfari masu neman aiki.
“Muna sanar da jama’a cewar babu wani daukar ma’aikata da hukumar gidajen gyaran hali zatayi.
“Saboda haka ya kamata jama’a su yi watsi da irin wadannan karairayi da ‘yan damfara ke shirya wa don cutar wanda bai jiba bai gani ba.
NAN
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com