37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Yan bindiga sun harbe wani dan kasuwa Inyamuri a jihar Kano

LabaraiYan bindiga sun harbe wani dan kasuwa Inyamuri a jihar Kano
20220925 081508
Mista Ifeanyi

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun harbe wani dan kasuwa dan kabilar Ibo mai suna Mista Ifeanyi a unguwar Sabon gari da ke Kano.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 8:45 na dare a Azubros Plaza, kusa da titin Faransa.

Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kan wanda sukazo harba sannan suka kada motar su sukayi gaba.

“A bayyane ya ke cewar sun zo ne don kashe Mista Ifeanyi wanda ya kasance Babban dillalin batira ne a garin Kano” inji wani ganau.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Kiyawa ba a samu jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Ƴan bindiga sun farmaki tawagar ɗan takarar gwamnan APC a Kaduna, sun sace jiga-jigan jam’iyyar

Ƴan bindiga sun sace wasu ƙusoshin jam’iyyar APC a jihar Kaduna a wani harin da ya auku akan hanyar Kaduna-Kachia a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa harin ya auku ne a wani waje da ake kira Tashar Icce wanda yake kusa da ƙauyen Kujama a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.

Tawagar ta su tana kan hanyar dawowa daga Kafanchan bayan kammala wani taron siyasa da shugabannin Kiristoci a ranar Alhamis.

Wani ɗan siyasa, wanda ya tsallake rijiya da baya a harin, ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan abu inda yake cewa kusan motoci biyar aka lalata. Yace ƴan bindigan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Ya kuma ce wasu daga cikin ƴan tawagar sun samu raunika yayin da aka yi awon gaba da mutum biyu.

Ɗan takarar gwamnan baya tare da tawagar lokacin da harin ya auku
Sai dai ɗan takarar gwamnan APC a jihar baya daga cikin tawagar waɗanda aka farmaka domin ya wuce Abuja daga Kafanchan.

Shugaban yaƙin neman zaɓen sa Sani Maina, Ahmed Maiyaki, wani ƙusa a jam’iyyar, da wasu tsirarun mutane sun tsira ba tare da samun raunika ba.

Jiga-jigan jam’iyyar da ƴan bindigan suka sace
Daga cikin waɗanda aka sace akwai ɗan takarar APC a kujerar majalisar jiha na Kajuru, Mr Madaki sannan da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Kajuru, Ruben Waziri.

Ben Maigari, ɗan’uwan mataimakin shugaban jam’iyyar ya tabbatar da aukuwar lamarin sannan yace har yanzu ƴan bindigan basu tuntuɓe su ba.

An kai musu hari, ƴan bindigan sun tare hanya sannan suka bude wuta akan tawagar da sauran motocin dake wucewa. An sace ɗan’uwana Ruben da Madaki saboda suna tare a cikin mota.

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe