27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Mun jinjinawa Osinbajo da Boss Mustapha bisa watsi da tikitin Muslim-Muslim na APC -Daniel Bwala

LabaraiMun jinjinawa Osinbajo da Boss Mustapha bisa watsi da tikitin Muslim-Muslim na APC -Daniel Bwala

Daniel Bwala, kakakin yaƙin neman takarar shugaban ƙasa na Atiku Abubakar, yace ya jinjinawa mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, bisa watsi da suka yi da tikitin Muslim-Muslim na jam’iyyar All Progressives Council (APC).

Maganar ta Daniel Bwala na zuwa ne bayan ba a saka sunayen Osinbajo da Boss Mustapha a cikin jerin sunayen mutanen da zasu jagoranci yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC. Jaridar The Cable ta rahoto.

Ba sunan Osinbajo cikin waɗanda zasu jagoranci yiwa jam’iyyar APC yaƙin neman zaɓe

Sunayen Osinbajo da Boss Mustapha basu fito a cikin jerin ƴan tawagar yaƙin neman zaɓen mai mambobi ɗari huɗu da ashirin da biyu (422).

Da yake magana kan lamarin, Daniel Bwala ya saki wani rubutu a shafin sa na Twitter ranar Asabar, inda yayi zargin cewa mutanen biyi sun buƙaci da kada a sanya su daga cikin tawagar.

Mun jinjinawa Farfesa Yemi Osinbajo da Boss Mustapha bisa ƙwarin guiwar su na yin fatali da tikitin Muslim Muslim ta hanyar buƙatar da kada a sanya su cikin masu yaƙin neman zaɓen APC. Ayi watsi da siyasar addini. Ƴan Najeriya za su raba tsakanin wuƙa da nama a wajen zaɓe.

Inji shi

Rashin ganin sunan Osinbajo dai ya tada ƙura inda wasu ke ganin cewa tsamin da alaƙa tayi a tsakanin sa da maigidan sa Tinubu ne ya sanya ba a saka sunan sa ba.

2023: Dalilin da ya sa aka cire sunan Osinbajo daga kwamitin yakin neman zaben Tinubu

A wani labarin na daban kuma, an bayyana dalilin da yasa aka cire sunan Osinbajo cikin masu jagorantar yaƙin neman zaɓen Tinubu.

Daraktan hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, Festus Keyamo, ya bayyana dalilin da ya sa aka cire sunan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo daga cikin ‘yan majalisar yakin neman zabe.

Mista Keyamo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, inda ya ce wannan matakine da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke da kansa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe