32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Yan bindiga sun hallaka mutane 15 a wani hari da suka kai masallaci a jihar Zamfara

LabaraiYan bindiga sun hallaka mutane 15 a wani hari da suka kai masallaci a jihar Zamfara
Armed Bandits 1140x570 1

Akalla mutum 15 ne suka ransa ransu wasu da dama suka jikkata a wani hari da aka kai wani masallaci a jihar Zamfara.

Kamfanin Dillacin Labarai ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Ruwan Jema da ke yankin karamar hukumar Bukkuyum a jihar, inda ‘yan bindigar a kan babura suka afkawa masallacin a yammacin ranar Juma’a suka fara harbi.

In ba a manta ba makonni uku kenan da aka sace wasu mutane suna tsaka da salla a masallacin juma’a da ke Zugu a garin na zamfara.

Ana tsammanin dai ‘yan bindigar na da sansani ne kusa da kauyen, shiyasa suka matsa musu da hare-hare.

Ƴan bindiga sun farmaki tawagar ɗan takarar gwamnan APC a Kaduna, sun sace jiga-jigan jam’iyyar

Ƴan bindiga sun sace wasu ƙusoshin jam’iyyar APC a jihar Kaduna a wani harin da ya auku akan hanyar Kaduna-Kachia a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa harin ya auku ne a wani waje da ake kira Tashar Icce wanda yake kusa da ƙauyen Kujama a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.

Tawagar ta su tana kan hanyar dawowa daga Kafanchan bayan kammala wani taron siyasa da shugabannin Kiristoci a ranar Alhamis.

Wani ɗan siyasa, wanda ya tsallake rijiya da baya a harin, ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan abu inda yake cewa kusan motoci biyar aka lalata. Yace ƴan bindigan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Ya kuma ce wasu daga cikin ƴan tawagar sun samu raunika yayin da aka yi awon gaba da mutum biyu.

Ɗan takarar gwamnan baya tare da tawagar lokacin da harin ya auku
Sai dai ɗan takarar gwamnan APC a jihar baya daga cikin tawagar waɗanda aka farmaka domin ya wuce Abuja daga Kafanchan.

Shugaban yaƙin neman zaɓen sa Sani Maina, Ahmed Maiyaki, wani ƙusa a jam’iyyar, da wasu tsirarun mutane sun tsira ba tare da samun raunika ba.

Jiga-jigan jam’iyyar da ƴan bindigan suka sace
Daga cikin waɗanda aka sace akwai ɗan takarar APC a kujerar majalisar jiha na Kajuru, Mr Madaki sannan da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Kajuru, Ruben Waziri.

Ben Maigari, ɗan’uwan mataimakin shugaban jam’iyyar ya tabbatar da aukuwar lamarin sannan yace har yanzu ƴan bindigan basu tuntuɓe su ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe