
Daraktan hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, Festus Keyamo, ya bayyana dalilin da ya sa aka cire sunan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo daga cikin ‘yan majalisar yakin neman zabe.
Mista Keyamo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, inda ya ce wannan matakine da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke da kansa.
“Ana ta yawo da wasu labarai ana kila akwai wata matsala data kunno kai cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sakamakon rashin fitar da sunan mataimakin shugaban kasa mai daraja, Farfesa Yemi Osinbajo, SAN, GCON. Sunan shi bai fito cikin jerin sunayen kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima ba.
“Domin kaucewa shakku, shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR, shine shugaban kwamitin yakin neman zaben. A saboda haka, shi ya ba da umarnin cewa kar a saka sunan mataimakin shugaban kasa da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a cikin kwamitin yakin neman zaben abar su,su mayar da hankali kan tafiyar da mulkin kasa da gudanar da mulki.
2023: Wike ya fasa ƙwai, ya bayyana tayin da Tinubu yayi masa don ya dawo APC
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana tayin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi masa domin ya dawo APC.
Gwamna Wike ya bayyana cewa Tinubu yayi masa tayin tikitin takarar ɗan majalisar dattawa domin ya dawo APC.
A kwanakin baya ne dai Tinubu da Wike suka gana a birnin Landan bayan rikicin jam’iyyar PDP ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Wasu daga cikin waɗanda suka faɗi a zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na jam’iyyar na yiwa kallon wanda har yanzu ya kasa hucewa daga zafin shan kayen da yayi.
Wike ya Magantu
Da yake magana a wani shirin talabijin ranar Juma’a, Wike yace:
Banyi takara ba domin na zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, ni ba irin sauran bane waɗanda suka siya fom ɗin sanata tare dana shugaban ƙasa, wannn yasa lokacin da yayi min tayin tikitin sanata, na ƙi karɓa.
Idan ina son mulki ko kasancewa cikin mulki da na karɓi tikitin sanatan. Amma sai nace aa. Wannan halin mutum ne wanda ya yarda da adalci da gaskiya. Saboda haka sharhin su bai yi daidai ba.
Bayan Tinubu wanda yake a APC, wasu sauran jam’iyyun sun yi magana dani har da Labour Party, saboda sun san ƙima ta da sanin yadda zan iya tabbatarwa sun lashe zaɓen 2023. Amma ban karɓi tayin da waɗannan jam’iyyun sukai min ba.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com