24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

“Mahaifiyata nake son taimako” Cewar yaro mai kuka yana aikin birkilanci

Labarai"Mahaifiyata nake son taimako" Cewar yaro mai kuka yana aikin birkilanci

Bidiyon wani yaro mai aikin ƙwadago na birkilanci ya sosa zuciyar mutane da dama.

A cikin bidiyon an nuna yaron yana a wajen aikin birkilanci yana aiki yana kuka.

Bayan bidiyon sa na farko ya karaɗe yanar gizo, wanda ya wallafa bidiyon mai suna Lukman Samsudeen, ya bayyana wasu abubuwan ban tausayi dangane da yaron mai suna Kamarudeen. Jaridar Yen.com.gh ta rahoto.

An bayyana wasu abubuwa game da rayuwar yaron

A wani sabon bidiyo da ya saka a TikTok, Lukman yace yaron yana zaune tare da shi kuma mahaifin sa ya rasu, yanzu haka maraya ne.

Lukman yace Kamorudeen yana aikin ne domin ya ga ya taimakawa mahaifiyar sa wacce manomiya ce.

Lukman, yaron yana ganin mahaifiyar sa sai ɗaya kawai a shekara cikin watan Disamba. Ya nemi mutane da su taimaki yaron, inda ya ƙara da cewa yaron yana son zuwa makaranta.

Kalli bidiyon a nan

Mutane sun tofa albarkacin bakin su

Abisoye ya rubuta:

Na ji tausayin sa, nima a da haka nake mai koyon aikin birkilanci. Amma yanzu ni mai gidan kai nane kuma ina da waɗansu a ƙasa na… Alihamdulila.”

Pes / fifa hub ya rubuta:

Omo nima na taɓa yin irin wannan rayuwar mai wahala a baya, amma yanzu kam sai godiya ga Ubangiji. Ya riga da ya zama tarihi.

Gara in yi kwadago a Nejeriya: Bidiyon dan Najeriya yana aikin wahala a kasar Dubai ya bayyana

A wani labarin na daban kuma, bidiyon wani ɗan Najeriya mai aikin ƙwadao a ƙasar Dubai ya bayyana, wasu sun ce gara suyi ƙwadago a Najeriya.

Wani dan Najeriya wanda bai dade da komawa Dubai ba ya bai wa ma’abota amfani da shafukan sada zumuntar zamani da dama mamaki, Legit.ng ta ruwaito.

A bidiyon an gan shi babu riga yana hada uwar zufa yayin da yake yunkurin tankwara tayoyi.

Yayin da mutane da dama ke yaba masa akan yadda yake halastaccen aiki, wasu kuma sun ja kunnensa akan yadda yake azabtar da kansa kafin tsufa ta zo ya rabu da lafiyarsa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe