37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

An cafke tsoho mai shekara 84 ya yiwa ƴar shekara 8 fyaɗe

LabaraiAn cafke tsoho mai shekara 84 ya yiwa ƴar shekara 8 fyaɗe

Hukumar ƴan sandan jihar Ogun tace ta cafke wani tsoho mai suna Stephen Jack, mai shekara 84 a duniya bisa zargin aikata fyade kan yarinya ƴar shekara 8 a jihar.

A cewar ƴan sandan, an cafke tsohon ne bayan mahaifin yarinyar ya kai rahoton lamarin a ofishin ƴan sanda. Jaridar The Cable ta rahoto.

Mahaifin yarinyar ya garzaya ofishin ƴan sandan ne bayan ya lura cewa yarinyar sa na zubar da jini a gabanta, sannan tace tsohon ne yayi mata fƴaɗe.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, yace binciken farko da akayi ya nuna cewa tsohon yayi ƙaurin suna wurin lalata ƙananan yara a unguwar Okun Owa, a Ijebu Ode.

Abinda sanarwar ta ƙunsa

An kama wanda ake zargin na rayuwa ne a unguwar Okun Owa dake Ijebu Ode, bayan mahaifin yarinyar ya shigar da ƙara babban ofishin ƴan sanda dake Obalende.

Mahaifin yarinyar ya kawo ƙarar cewa yarinyar sa na zubar da jini a gabanta, sannan da ya tambaye ta dalilin hakan sai tace wanda ake zargin ne yayi lalata da ita.

Bayan karɓar ƙarar, nan take DPO na Obalende, SP Murphy Salami, ya tura jami’an sa zuwa wurin inda suka cafke tsohon.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa tsohon yayi ƙaurin suna wajen lalata da ƙananan yara a yankin.

Inji shi

Opeyemi ya kuma bayyana cewa an kai yarinyar zuwa babban asibitin Ijebu Ode domin duba lafiyarta.

Yan sanda sun cafke wani matashi bisa laifin yiwa tsohuwa ‘yar shekara 75 fyaɗe

A wani labarin na daban kuma, an kama wani matashi bisa laifin yiwa tsohiwa ƴar shekara 85 fyaɗe

Yan sanda a jihar Anambra a ranar Asabar sun cafke wani mutum mai shekara 30 a duniya bisa zargin yin fyaɗe ga wata tsohuwa mai shekaru 75 a duniya.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Asabar a birnin Awka.

Yace wanda ake zargin, wanda ɗan asalin ƙauyen Eyiba ne a jihar Ebonyi, an cafke shine da misalin ƙarfe 4 na yamma ranar Juma’a a ƙauyen Nkwelle Awkuzu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe