Ƴan bindiga sun sace wasu ƙusoshin jam’iyyar APC a jihar Kaduna a wani harin da ya auku akan hanyar Kaduna-Kachia a jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa harin ya auku ne a wani waje da ake kira Tashar Icce wanda yake kusa da ƙauyen Kujama a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.
Tawagar ta su tana kan hanyar dawowa daga Kafanchan bayan kammala wani taron siyasa da shugabannin Kiristoci a ranar Alhamis.
Wani ɗan siyasa, wanda ya tsallake rijiya da baya a harin, ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan abu inda yake cewa kusan motoci biyar aka lalata. Yace ƴan bindigan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi.
Ya kuma ce wasu daga cikin ƴan tawagar sun samu raunika yayin da aka yi awon gaba da mutum biyu.
Ɗan takarar gwamnan baya tare da tawagar lokacin da harin ya auku
Sai dai ɗan takarar gwamnan APC a jihar baya daga cikin tawagar waɗanda aka farmaka domin ya wuce Abuja daga Kafanchan.
Shugaban yaƙin neman zaɓen sa Sani Maina, Ahmed Maiyaki, wani ƙusa a jam’iyyar, da wasu tsirarun mutane sun tsira ba tare da samun raunika ba.
Jiga-jigan jam’iyyar da ƴan bindigan suka sace
Daga cikin waɗanda aka sace akwai ɗan takarar APC a kujerar majalisar jiha na Kajuru, Mr Madaki sannan da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Kajuru, Ruben Waziri.
Ben Maigari, ɗan’uwan mataimakin shugaban jam’iyyar ya tabbatar da aukuwar lamarin sannan yace har yanzu ƴan bindigan basu tuntuɓe su ba.
An kai musu hari, ƴan bindigan sun tare hanya sannan suka bude wuta akan tawagar da sauran motocin dake wucewa. An sace ɗan’uwana Ruben da Madaki saboda suna tare a cikin mota.
Jiragen yaƙin NAF sun sake yin luguden wuta a sansanin wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga a Zamfara
A wani labarin na daban kuma, jiragen yaƙin sojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a sansanin wani shugaban ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Rundunar sojojin saman Najeriya ta sake yin luguden wuta a sansanin wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Jiragen yaƙin rundunar sun yi luguden wuta a sansanin ƙasurgumin ɗan bindiga, Dan-Karami, a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com