24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Abin takaici: An gudu an bar wani jariri a asibiti a jihar Jigawa

LabaraiAbin takaici: An gudu an bar wani jariri a asibiti a jihar Jigawa

Wani abin ban takaici da jimami ya auku a jihar Jigawa, inda aka tafi aka bar wani jaririn yaro a cikin wani asibiti.

An dai bar jaririn yaron wanda yake da ƙwana ɗaya a duniya, a cikin babban asibitin Kazaure, a ranar Alhamis, 22 ga watan Satumban 2022. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Hukumar ƴan sanda ta tabbatar da barin jaririn

Kakakin hukumar ƴan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Kakakin na hukumar ƴan sandan ya bayyana cewa darektan babban asibitin na Kazaure, ya miƙa jaririn a hannun jami’an jindaɗin jama’a na ƙaramar hukumar.

Ya kuma ƙara da cewa tuni har wasu mata guda biyar sun ce a basu jaririn domin su shayar da shi.

Shiisu yayi nuni da cewa an yaba sosai da kulawar da suka nuna inda akayi alƙawarin tantance su.

“Bayan an kammala tantance su, za a ba ɗaya daga cikin su ta shayar da jaririn” A cewar DSP Shiisu.

Iyayen budurwa sun fatattake ta bayan ta haifa musu jaririn balarabe daga dawowa Saudiyya yin aikatau

A wani labarin na daban kuma, iyayen wata budurwa sun fatattake ta bayan ta haifa musu jaririn balarabe bayan ta dawo aikatau daga ƙasar Saudiyya.

Jama’a sun tallafawa wata budurwa wacce iyayenta suka fatattaketa bayan ta haifa musu jaririn balarabe bayan ta dawo daga Saudiyya, Legit.ng ta ruwaito.

Kamar yadda wata Judy Oricho mai tallafawa masu kananun karfi ta bayyana a shafinta na Facebook, wanda Anna Awuor mai shekaru 29 ta fuskanci cin zarafi ne daga wanda take aiki karkashinsa, daga nan ta samu ciki.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe