31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Iyayen saurayina na barin gidanmu don sa ranar aurenmu, an tasa min wanke-wanke, Budurwa

LabaraiIyayen saurayina na barin gidanmu don sa ranar aurenmu, an tasa min wanke-wanke, Budurwa

Wata kyakkyawar budurwa ta koka akan yadda aka tasa mata kayan wanke-wanke a gidansu bayan ‘yan uwan saurayinta sun je gidansu an sa ranar aurenta da shi, Legit.ng ta ruwaito.

Budurwar mai amfani da suna @meetlauretta ta ce bata dade da gama shagalin da sa ranar aurenta ba sai aka tasa mata kayan wanke-wankan da ‘yan uwan saurayinta su ka bata don wanke.

Bidiyon ya bayyana yadda ta zauna tayi tagumi tare da tsibin wanke-wanke a gabanta. Ta kuma bayyana yadda aka sa ta debo ruwa kasancewar ita ce autar gidansu ba ta kanni.

Kamar yadda ta bayyana:

“Jiya ne da aka sa ranar aurena. Amma kasancewar ni ce auta a gidanmu sai ga shi an tasa min dibar ruwa da kuma wanke-wanke.”

Tsokacin mutane karkashin bidiyon

Nan da nan ‘yan Najeriya su ka jajanta mata.

@lukesyntyche tace:

Haka da aka yi min kasancewar jiya aurena. Da karfe 7 na safiyar Yau aka aike ni siyo barkono saboda wanda aka siyo bai isa ba.”

ebundia tace:

Haka ne fah, nima haka su ka wanke kwanuka sannan aka sa ni in jera kwanukan a kicin daga nan na fadi kasa.”

monalisa2227 tace:

Haka nima aka yi min jiya.”

Smartb65 tace:

Da wa zai wanke miki kwanukan?

Nayi nadamar rashin yin saurayi a rayuwata -Tsohuwa ƴar shekara 92 ta koka

Wata tsohuwa mai shekara 92 a duniya, Xaveline, daga ƙasar na rayuwar kadaici sannan babban dana sanin ta a rayuwa shine rashin samun saurayin da zai aure ta.

Tsohuwar matar dai na da ƴan’uwa 14 waɗanda duk sunyi aure sun ƙyale ta a gida.

Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa tsohuwar ta shaidawa tashar Afrimax a Youtube cewa:

Na rayu tare da iyaye na, sun sha gayamin cewa suna jiran ranar da zanyi aure na samar musu da jikoki.

Nima na so hakan, amma abin takaicin sun rasu banyi aure ba kuma kamar nayi tsufa da na samu saurayi.

Na zama saura ni kaɗai kawai hakan ya sanya na yanke shawarar komawa wurin ƴar autar mu.

Wasu daga cikin ƴan’uwa, abokai da makwabta na ganin cewa kamar maita na da hannu a rashin auren da tsohuwar tayi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe