31.5 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

2023: Wike ya fasa ƙwai, ya bayyana tayin da Tinubu yayi masa don ya dawo APC

Labarai2023: Wike ya fasa ƙwai, ya bayyana tayin da Tinubu yayi masa don ya dawo APC

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana tayin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi masa domin ya dawo APC.

Gwamna Wike ya bayyana cewa Tinubu yayi masa tayin tikitin takarar ɗan majalisar dattawa domin ya dawo APC.

A kwanakin baya ne dai Tinubu da Wike suka gana a birnin Landan bayan rikicin jam’iyyar PDP ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Wasu daga cikin waɗanda suka faɗi a zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na jam’iyyar na yiwa kallon wanda har yanzu ya kasa hucewa daga zafin shan kayen da yayi.

Wike ya Magantu

Da yake magana a wani shirin talabijin ranar Juma’a, Wike yace:

Banyi takara ba domin na zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, ni ba irin sauran bane waɗanda suka siya fom ɗin sanata tare dana shugaban ƙasa, wannn yasa lokacin da yayi min tayin tikitin sanata, na ƙi karɓa.

Idan ina son mulki ko kasancewa cikin mulki da na karɓi tikitin sanatan. Amma sai nace aa. Wannan halin mutum ne wanda ya yarda da adalci da gaskiya. Saboda haka sharhin su bai yi daidai ba.

Bayan Tinubu wanda yake a APC, wasu sauran jam’iyyun sun yi magana dani har da Labour Party, saboda sun san ƙima ta da sanin yadda zan iya tabbatarwa sun lashe zaɓen 2023. Amma ban karɓi tayin da waɗannan jam’iyyun sukai min ba.

Ku taimaka ku taya ni da kamfen, Atiku ga Wike da sauran ƴan takarar PDP da ya kayar

A wani labarin na daban kuma, Atiku ya nemi ƴan takarar da ya kayar da su taimaka su taya shi wurin yin yaƙin neman zaɓe.

Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nemi taimakon abokan takararsa na zaben fidda gwani don su taya shi aikin da jam’iyyarsu za ta samu nasara, Pulse.ng ta ruwaito.

Abubakar ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi da safe a Abuja a matsayin jawabinsa bayan ya samu nasarar lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP din.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe