24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Jama’a sun sha mamaki bayan matashi bayyana wa ‘yan TikTok ainihin fuskarsa babu ‘filter’

LabaraiJama'a sun sha mamaki bayan matashi bayyana wa ‘yan TikTok ainihin fuskarsa babu ‘filter’

Mutane da dama sun sha mamaki bayan ganin bidiyon wani matashi bayan ya cire filter daga wayarsa. A bidiyon mai ban dariya, an ga yadda wani @roydampz ya bayyana cewa yana so ya nuna wa kowa asalin fuskarsa, Legit.ng ta ruwaito.

Da farko an ga yadda yayi haske ya kuma yi gunin birgewa, daga karshe kuma an ga yadda yayi bakikkirin.

Yanayin sauyawar da kalar fatarsa tayi ya bai wa mutane da dama mamaki, amma mutumin ya yi bayani dalla-dalla.

Ya ja kunnen wadanda su ke mato masa akan su kiyaye, ga asalin yadda halittarsa take.

Nan da nan mutane su ka fara tsokaci a karkashin bidiyon:

@Classic_contour_gh yace:

Kun ga irin filtar da yawancin sanannun mutanen TikTok ke amfani da ita, sai ayi ta tambayarsu irin man da suke shafawa.”

@joychidera199 tace:

Duk da haka ka yi kyau.

Laudina7676 tace:

Wanene ban da ni yayi mamaki.”

@adomklans yace:

Kamar mutane biyu na daban-daban.”

@Queen-Feli tace:

Sai da nayi ihu nace wannan wacce irin rayuwa ce.”

Bella tace:

Amma ba laifi kana da kyau.

@Mimi Bea465 tace:

Ina nan ina gyada kai na.”

@OBO yace:

Kamar ba shi bane, mutane biyu ne mabanbanta.”

Tabarar da mata masu yabon ma’aiki ke yi ta zarce ta masu rawar TikTok da ‘yan fim, Fantimoti

Fitacciyar mawakiyar finafinai a baya, yanzu haka kuma sha’ira a fannin yabon manzon Allah SAW, Maryam Fantimoti ta ce tabarar da mata sha’irai masu yabon ma’aiki su ke yi, ta fi ta ‘yan rawar TikTok da ‘yan fim.

Kamar yadda ta shaida wa Freedom Radio Kano, ta ce dangane da shigarsu ta fitar da surarsu, cakudewa tsakanin maza da mata da suke yi ya munana.

A cewarta:

Abinda yasa nayi magana akan na hadarar manzon Allah SAW shi ne yadda ake yawan korafi akan yabon manzon Allah a gyara. Na daya a gyara alkaluma. Na biyu a gyara harshe, sannan a gyara dabi’a ta sha’irai.

Saboda mu mata ne. Wata sha’irar idan ki ka kalleta sa’ar ‘yar da na haifa ce. Za ki samu ta yi shiga irin ta su ta yara.

Ya kamata a gyara. Ina ganin kuma duk abinda ake yi yayin yabon manzon Allah SAW in dai ya saba wa dabi’a to ina tunanin wannan abin ya yi muni.

A bangaren wata sha’irar ta ce sam ba haka bane. Bai dace a yi wa sha’irai kudin goro ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe