31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Yanzu -yanzu: Wani gini ya sake ruftawa a garin Legas

LabaraiYanzu -yanzu: Wani gini ya sake ruftawa a garin Legas
9A4EB7DF 11C2 4363 993F F32A1B3E1794 1040x570 1
Gini ya rugujeca jihar Legas

Wani gini a kan titin Sonuga, Palm Avenue, a yankin Mushin da ke garin Lagos, ya ruguzo.

Kakakin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, Nosa Okunbor ya tabbatar wa jaridar PREMIUM TIMES faruwar lamarin a yau Juma’a.

Inda Ya bayyana cewa suna kan hanyarsu ta zuwa wurin da lamarin ya faru za su bada cikakken bayani daga baya.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a iya tantance adadin benayen ginin da ya ruguje ba kuma ba a san ko akwai mutanen da abun ya rutsa da su ba.

Mufti Ismail Menk ya garzaya Pakistan domin taimakawa mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su

Sanannen malamin addinin musuluncin nan Mufti Ismail Menk, yanzu haka yana ƙasar Pakistan domin taimakawa mutanen da iftila’in ambaliyar ruwa ta ritsa da su.

Yanzu haka yana a Sindh domin bada agajin gaggawa ga mutanen da mummunar ambaliyar ruwan ta ritsa da su. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

A shafin sa na Instagram, Mufti Menk ya sanya wani bidiyo wanda ya nuna shi yana ziyartar inda ambaliyar ruwan ta shafa a Sindh, Jhuddo.

A wani kira da yayi ga mabiyan sa, Mufti Menk ya roƙe su da su taimakawa mutanen da abin ya ritsa da su.

A wata wasiƙar da ya fitar ya bayyana cewa:

Lamarin ya ta’azzara! Ana buƙatar mu a Pakistan! Ku taimaka da tantuna. Ku taimaka wurin kawo agaji a rayuwar iyalai ta hanyar samar musu da jin ƙai! Akwai tantuna kan farashin £100 kowane! Akwai buƙatar neman agaji nan da wasu shekaru masu zuwa.

Mufti Ismail Menk ya shahara sosai
Mufti Ismail Menk sananne kan fahimtar sa ta koyarwar addinin musulunci. Mufti Ismail Menk yana da sama da mutum miliyan ɗaya masu bibiyar sa a shafin Facebook domin shawarwarin sa kan yin rayuwa mai kyau.

Yana kuma sanya bidiyoyi a Youtube lokaci bayan lokaci kan darussan musulunci da kuma kuma abubuwan dake faruwa da suka shafi musulmai a duniya gabaɗaya.

Mufti Ismail Menk malami ne, mai wa’azi kuma ɗan gwagwarmaya wanda aka haifi a birnin Kaduna a tarayyar Najeriya. Shine kuma ya kafa gidauniyar Islamic Mission Foundation, wacce ke da rassa a sama da ƙasashe 30 a duniya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe