27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Cutar kwalara ta yi sanadiyyar mutuwar mutane Goma a jihar Gombe

LabaraiCutar kwalara ta yi sanadiyyar mutuwar mutane Goma a jihar Gombe
IDP water
Ruwa mara tsafta ke haifar da cutar kwalara

Jihar Gombe ta sanar da bullar cutar kwalara tare da mutuwar mutane akalla goma a fadin jihar.

Kwamishinan lafiya na Gombe, Habu Dahiru ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Gombe yayin da yake jawabi ga manema labarai kan bullar cutar a jihar.

Mista Dahiru, wanda ya samu wakilcin Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Gombe, Abdulrahman Shuaibu, ya ce ya zuwa ranar 20 ga Satumba, adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu zuwa 236.

Ya ce a shekarar 2021, jihar ta samu adadin mutane 2,373 da suka kamu da cutar.

“A wannan shekarar, daga watan Yuni, mun sami bullar cutar kwalara a karamar hukumar Balanga kuma saboda shirin gaggawa da ya wakana; An yi nasarar dakile barkewar cutar.

“An samu karuwar ruwan sama da ambaliyar ruwa a sassa da dama na jihar wanda hakan ya haifar da barkewar cutar kwalara.

“An samu bullar cutar a unguwanni takwas a fadin kananan hukumomin Balanga, Yamaltu-Deba, Nafada, Funakaye da fadin kwaryar jihar.

“Ma’aikatar Lafiya ta Jiha ta fara aiwatar da ayyukan kiwon lafiyar jama’a cikin gaggawa don rigakafi da shawo kan cutar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe