Rundunar sojojin saman Najeriya ta sake yin luguden wuta a sansanin wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Jiragen yaƙin rundunar sun yi luguden wuta a sansanin ƙasurgumin ɗan bindiga, Dan-Karami, a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Majiyoyi sun shaidawa jaridar The Punch cewa ƴan bindiga da dama sun rasa rayukan su lokacin da akayi luguden wuta kan sansanin ranar Alhamis.
Wani mazaunin yankin, Musa Shehu, yace ya hango hayaƙi daga can nesa yana fitowa daga sansanin na ƴan bindigan.
Sojojin sama ne suka yi luguden wuta a sansanin da yammacin nan (ranar Alhamis), sannan mun hango hayaƙi yana tashi daga wurin.
Shehu ya kuma bayyana cewa sun jiyo ƙarar tashin bamai-bamai lokacin da jiragen yaƙin sojojin saman suke luguden wuta a sansanin na Dan-Karami
Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, ba samu tabbacin cewa ko Dan-Karami yana daga cikin ƴan bindigan da suka halaka ba a cikin harin.
Dan-Karami wani ƙasurgumin ɗan bindiga ne wanda ya addabi mutanen jihohin Zamfara da Katsina.
A cIkin ƴan kwanakin nan dai dakarun rundunar sojin sama ta Najeriya sun ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a sansanin ƴan bindiga, a ƙoƙarin da suke na murƙushe su domin kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta addabi mutanen jihohin Arewa maso Gabas, inda matsalar tsaron tafi ta’azzara.
Ƴan bindiga da dama sun halaka bayan sojin sama sun yi luguden wuta sansanin Bello Turji
A wani labarin na daban kuma ƴan bindiga da dama sun halaka bayan sojojin sama sun farmaki samsanin Bello Turji a jihar Zamfara.
Rundunar sojin saman Najeriya tayi luguden wuta a sansanin riƙaƙƙen ɗan ta’adda Bello Turji, a ranar Asabar a jihar Zamfara, inda ta hari wasu daga cikin na hannun daman sa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba a samu cikakkun bayanai ba dangane da harin amma jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ƴan bindiga da dama sun halaka a harin.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com