27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Sarauniyar Ingila Elizabeth II tafi wasu musulman da dama a wurina -Adamu Garba

LabaraiSarauniyar Ingila Elizabeth II tafi wasu musulman da dama a wurina -Adamu Garba

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Adamu Garba, yayi ƙarin haske kan maganar da yayi akan sarauniyar Ingila Elizabeth II.

A ranar Litinin da ta gabata ne dai akayi bikin binne gawar sarauniyar ta Ingila bayan mutuwarta. Sarauniyar dai ta mutu tana da shekara 96 a duniya.

Adamu Garba ya janyo cece-kuce

A wata magana da ta janyo cece-kuce Adamu Garba, yace yayi mafarkin cewa yaga sarauniyar ta Ingila a Aljannah a cikin mafarkin sa.

Wannan maganar da yayi ta sanya mutane da dama sun yi masa raddi don ganin rashin dacewar maganar a mahanga ta addinin musulunci.

Sai dai Adamu Garba ya fitar da wani bidiyo inda yayi ƙarin haske kan maganar da yayi. A cikin bidiyon ya bayyana cewa mutane sun cika shishshigi kan lamuran Ubangiji.

Ya kuma bayyana cewa sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu tafi wasu musulman da yawa a wurin shi masu ganin cewa sun fi kowa tsarki.

A kalaman sa:

Kai jama’a, kuma dai mutane an cika shishshigi wallahi, ina ruwanka da tsarin Allah, ina ruwanka da al’amarin Allah, ina ruwanka da rahamar da Allah yaso ya ɗorawa bawan sa kowane ne shi.

Nifa a nawa ganin wannan Elizabeth ɗin ma tafi musulmai da yawa, da yawa daga cikin musulmai da suke nuna kansu a matsayin sun fi kowa tsarki bayan Allah (SWT) ya gaya mana da mu daina aibanta kanmu mu daina tsarkake kanmu.

Ga dai cikakken bidiyon nan ƙasa wanda Kannywood Celebrities suka sanya a shafin su na Facebook.

Kalli bidiyon a nan

Jimamin mutuwa: Naira Marley yayi zanen fuskar sarauniyar Ingila a hannun sa

A wani labarin na daban kuma, Naira Marley yayi zanen fuskar sarauniyar Ingila a hannun sa.

Shahararren mawaƙin nan na Kudancin Najeriya, Azeez Adeshina Fashola wanda akafi sani da Naira Marley, yayi ta’aziyyar rasuwar sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II.

Naira Marley ya garzaya shafukan sada zumunta inda ya nuna sabon zanen da akayi masa a jikin sa domin nuna girmamawa ga sarauniyar ta Ingila wacce ta riga mu gidan gaskiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe