27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Ƴan sandan Isra’ila sun tsare darektan masallacin Al-Aqsa

LabaraiƳan sandan Isra'ila sun tsare darektan masallacin Al-Aqsa

Ƴan sandan ƙasar Isra’ila sun kama tare da tsare darektan masallacin Al-Aqsa, Sheikh Omar Kiswani.

Jaridar The Islamic Information ta ambato wakilin jaridar WAFA na cewa, ƴan sandan sun cafke malamin sannan suka tsare shi har na zuwa wani lokaci.

Kamar yadda majiyoyi suka bayyana, ƴan sandan sun kwace na’ura mai ƙwaƙwalwa da wasu takardu na Sheikh Kiswani a gidan sa bayan sun yi wa gidan binciken ƙwaƙwaf.

Dalilin da yasa ƴan sanda suka kama Sheikh Omar Kiswani

An tsare shi a wani ofishin ƴan sanda na sa’o’i da dama kafin a sake shi.

Ana tunanin cewa an tsare Sheikh Kiswani ne saboda barazanar da Isra’ila ke yiwa jami’ai da ƴan gwagwarmayan dake kiran da ayi zaman dirshan a masallacin na Al-Aqsa.

Yahudawan Isra’ila na son gudanar da bukukuwan al’ada a masallacin Al-Aqsa

A wani keta haddin tsarin da ya daɗe wanda ya ayyana masallacin Al-Aqsa a matsayin wurin ibadar da musulmai kaɗai ke da hurumin yin ibada a ciki, masu tsananin kishin addinin Yahudanci suna son kutsawa cikin masallacin a lokacin bukukuwan Yahudawa domin gudanar da abubuwan al’ada.

A cikin kwanakin nan da suka shuɗe, an tsare Palasɗinawa da dama a Jerusalem ta Gabas, yayin da wasu kuma aka basu umurnin kada su zo kusa da masallacin Al-Aqsa.

Kasar Saudiyya ta damke mutumin da ake zargi da taimakawa dan jaridar kasar Isra’ila shiga garin Makka

A wani labarin na daban kuma, Ƙasar Saudiyya ta cafke wani mutum da ya taimakawa ɗan jaridar ƙasar Isra’ila shiga garin Makkah.

An kama wanda ake zargi da taimakawa wajen shigar da dan jarida da ba musulmi ba cikin birnin Makkah mai tsarki, wanda hakan ya sabawa dokar haramta wa wadanda ba musulmi ba shiga garin.

Jami’an Saudiyya sun sanar a ranar Juma’a cewa dan jaridar kasar Isra’ila Gil Tamari, wanda ya je Saudiyya don bayar da rahotannin ziyarar da shugaban Amurka Joe Biden ya kai a can, ya yi amfani da damar don shiga masarautar, ya shiga cikin birnin Makkah, ya yi zagaya tare da watsawa gidan talabijin na Channel 13.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe