
Hukumar kula da gidajen gyaran Hali ta Najeriya, NCoS, ta gargadi masu neman aikin yi da su kula da kyau don gudun fadawa hannun ‘yan damfara, hukumar ta ce labarin cewar ta fara atisayen daukan ma’aikata karyane
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Umar Abubakar shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a yau Alhamis a garin Abuja.
Mista Abubakar ya ce Dolene su fito su gayawa jam’a don rage tasirin kokarin da ‘yan damfara ke yi na cuta ga masu neman aiki.
“Ma’aikatar ta samu labarin cewar an fitar da tallar karya na daukar ma’aikata.
“Wasu marasa kishin kasa ne ke yin wannan aikin dan su damfari masu neman aiki.
“Muna sanar da jama’a cewar babu wani daukar ma’aikata da hukumar gidajen gyaran hali zatayi.
“Saboda haka ya kamata jama’a su yi watsi da irin wadannan karairayi da ‘yan damfara ke shirya wa don cutar wanda bai jiba bai gani ba.
NAN
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com