27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Da ayar Al’Qur’ani na gamsar da mahaifina har ya amince na fara fim, Jarumi Nura Hussaini

LabaraiKannywoodDa ayar Al’Qur’ani na gamsar da mahaifina har ya amince na fara fim, Jarumi Nura Hussaini

Jarumin finafinan Kannywood, Nura Hussaini ya bayyana yadda aka yi ya gamsar da mahaifinsa har ya amince ya bar shi ya fara harkar fim.

A wata tattauna da BBC Hausa tayi da shi a shirin Daga Bakin Mai Ita, ya ce sai da ya janyo wa mahaifinsa ayar Al’Qur’ani wacce ta yi magana akan fadakarwa sannan ya amince.

Ya fara bayyana cewa mahaifinsa malami ne kuma a wurinsa yayi karatun addini har ta kai ga ya yi sauka sannan ya fara hadda.

Sannan a wurin mahaifiyarsa ya koyi littafan addini da dama. Ya bayyana yayi karatun boko a Kano bayan tasowa a garin Kano.

Ya ce a baya shi malamin Islamiyya ne don yana koyar da yara karatu. A ranar da ya fara ganin fim ne ya fara sha’awar shirin, a lokacin ya je koro yara don tafiya islamiyyarsa da yake yi tsakanin magriba da isha.

Ganin yadda ake shirin fim din “Kara da Kiyashi” yasa yayi sha’awar shirin daga nan ya nemi sanin yadda abin yake.

Yayin gamsar da mahaifinsa ya fara da cewa:

Ina tsoron kada mahaifina ya ki amincewa in yi saboda zai ga cewa fim abu ne mai cinye lokacin karatu. Nace Malam na ga wani abu da ake yi wai shi fim. Kuma ina so in fara.

Amma bai gane ba saboda be ma san menene shi ba. Sai nace abinda ake nufi da fim shi ne ud’u ila sabili Rabbika bil hikmati wal mau’idhatil hassanati.

Sai yayi shiru, yace, ai wannan abu mai kyau ne. To sai naji dadi saboda abinda nake so shi ne in ji ya amsa.”

Ya ci gaba da bayyana yadda mahaifinsa yayi masa wasiyya da ya kasance mai tsare mutuncin kansa kamar yadda iyayensa su ka tsare nasa.

Matsayin da na ba mahaifina na gida, shi na bai wa Adam Zango, Jaruma Tumba Gwaska

Bayan wani gidan talabijin na FarinWata ya yi hira da jaruma Tumba Gwaska, an tambayeta akan yadda take da alaka mai karfi tsakaninta da Jarumi Adam A. Zango har wasu suke ganin kamar soyayya ce tsakaninsu, kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Sai dai a bayaninta, ta tabbatar da cewa babu soyayya tsakaninsu, Uban gidanta ne shi sannan matsayin uba yake a wurinta kuma akan shi sai inda karfinta ya kare.

Kamar yadda ta ce:

“To a gaskiya dai babu komai tsakanina da Baba Ado, Wallahi Wallahi babu komai tsakanina da Adamu sai mutunci. Yadda na dauki girma na ba mahaifina na gida, haka na dauka na ba Adam.

“Uban gidana ne shi, ina ji da shi, ina alfahari da shi kuma sai inda karfina ya kare akanshi saboda ai dan halak shi ake yi wa halacci inji bahaushe.”

Yayin da aka tabo ma Tumba batun Safara’u wanda tace musu ‘yan wahala, ta ce kowa yayi nagari don kansa.

Ta ce fim ne ya sanya Safara’u yin suna sannan babu yadda za ayi mutane su kalleta idan banda fim din da ya fito da ita.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe