
Akalla mutane 25 ciki har da mayakan Boko Haram 20 da suka mika wuya ne suka rasa ransu sakamakon barkewar cutar kwalara a sansanin Hajji inda a yanzu haka kimanin tubabbu 12,000 ne aka maidasu garin Maiduguri.
An gano cewa akalla mutane bakwai ne suka mutu a ranar Talata, inji rahoton Daily Trust. Wakilin Daily Trust ya tattaro cewa an samu wasu karin muutun 14 da suka kamu da cutar a sansanin Hajji a ranar Laraba.
A cewar wata majiya, ma’aikatan lafiya tare da goyon bayan kungiyoyi masu zaman kansu da kuma hukumar lafiya ta duniya suna fafutukar shawo kan matsalar mace-macen.
Cewar sanarwar: “Akalla tubabbun ‘yan boko haram 20 ne suka mutu sakamakon bullar cutar kwalara a sansanin aikin Hajji sannan wasu hudu sun mutu a sansanin Bama.
Har ila yau, rahotanni sun kara bayyana cewa wasu uku sun mutu a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Garage Muna.
Kusan mutane 1,000 ne suka kamu da cutar ya zuwa yanzu, kuma a halin yanzu daruruwa suna karbar magani a cibiyoyin lafiya daban-daban,” inji majiyar.
Moreso, wani babban jami’in ma’aikatar lafiya da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya bayyana cewa tubabbun ‘yan Boko Haram 11 ne kawai da wasu mutane uku a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Garage da cutar kwalar ta kashe ba mutum 20 ba.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-