Wani dan Najeriya wanda bai dade da komawa Dubai ba ya bai wa ma’abota amfani da shafukan sada zumuntar zamani da dama mamaki, Legit.ng ta ruwaito.
A bidiyon an gan shi babu riga yana hada uwar zufa yayin da yake yunkurin tankwara tayoyi.
Yayin da mutane da dama ke yaba masa akan yadda yake halastaccen aiki, wasu kuma sun ja kunnensa akan yadda yake azabtar da kansa kafin tsufa ta zo ya rabu da lafiyarsa.
Mutane da dama su na kallon Dubai a matsayin wurin da kudi yake yawo tamkar ruwa. Sai dai mutumin ya gwada musu cewa duk da yadda ake kallon wurin, ba kowa bane yake jindadi.
Tsokacin wasu mutane karkashin bidiyon
Nan da nan mutane su ka hau tsokaci karkashin bidiyon. Ga wasu daga ciki:
Mc Daniel yace:
“Gara in yi wahalar a gida.”
Benjamin Stewart yace:
“Chapdi, gaskiya ba zan iya ba.”
Chibuzoraj yace:
“Yadda ku ke lankwasa taya a Dubai da wahala. Idan da zan gwada maka yadda mu ke yin tamu da ka gane ta fi sauki.”
Rebby tace:
“Zan ce Ubangiji ya sanya albarka a nemanka. Ya cika maka burinka na alkhairi.”
Sabbin hotunan Maryam Yahaya a Dubai babu rigar mama sun janyo mata zagi
A ranar Juma’a, 18 ga watan Fabrairun 2022 jarumar Kannywood, Maryam Yahaya ta saki sabbin hotunan ta a shafin ta na Instagram ba tare da ta sanya rigar mama ba.
Hotunan sun janyo mata suka da caccaka ko ta ina kafar inda wasu suka dinga zagin ta akan yadda bata dade da murmurewa daga ciwo ba ta fara shigar banza.
Wasu sun dinga yi mata wa’azi suna cewa ya kamata ta yi wa kanta fada ta daina duk wasu ayyuka marasa kyau musamman ganin ko jikin ta bata gama mayarwa ba.
A kwanakin baya jarumar ta yi ciwo wanda mutane da dama suka zaci mutuwa zata yi don duk ta rame ta fita hayyacin.
A lokacin, masoyanta sun dinga yi mata fatan alkhairi da kuma fatan zata natsu, ciwon ya zama izina a gare ta ta gyara rayuwar ta.
Ba wannan bane karon farko da jarumar ta saba yin hotuna ba tare da ta sanya rigar mama ba. Ga masu bibiyarta a Instagram, ta kan saki bidiyoyi ko kotuna sanye da riguna da suke tabbatar da hakan.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com