27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

An fi samun matasa masu tsula fitsarin kwance a Afirka fiye da sauran nahiyoyi, Bincike

LabaraiAn fi samun matasa masu tsula fitsarin kwance a Afirka fiye da sauran nahiyoyi, Bincike

Wani likita da ke Jihar Kano mai suna Dr Kabir Auwal Yusuf ya bayyana yadda a wani bincike da cibiyar samar da bayanan lafiya ta gudanar ya tabbatar da cewa bakaken fata ‘yan Afirka ne su ka fi yin fitsarin kwance idan sun girma, Dala FM ta ruwaito.

Kamar yadda ya bayyana a wani taro na musamman da aka gudanar a wani asibiti mai zaman kansa da ke Jihar Kano, ya ce hakan yana da alaka da sakacin bakaken fatar.

Ya shaida yadda tun farko matsalar daga kwakwalwar mutum take zuwa, kasancewar ba ta kai sakon cewa mutum na jin fitsari idan yana bacci wanda hakan ke ba shi damar yi a kwance.

A cewarsa ‘yan Afirka na da sakaci a bangaren lafiya don ba sa yawan zuwa ganin likita akai-akai har sai komai ya tsananta. Yayin jin ra’ayoyin jama’a, akwai wadanda su ka alakanta hakan da yanayin cimarmu.

Wasu sun ce rashin kulawa ne ta yadda su ke kin yin fitsarin a falke har sai ya matse su, daga nan sai ta kai su ga yin na kwance.

Matata ta tsinka min mari ina tsaka da fallasa yadda take tara fitsari a uwar-daka a gidan rediyo

Wata mata ‘yar kasar Ghana ta nuna fushinta lokacin da ta dauke mijinta da mari bayan ya bayyana yadda ta ke tara fitsari a gaban dan jaridan m gidan rediyon Nhyira FM.


Gidan rediyon a yankin Ashanti yake a cikin kasar Ghana.

Ta ci zarafin mijinta a gaban dan jaridar, mai gidansu da sauran bakin da aka gayyata don tattaunawa da su.


Ya fallasa yadda ta ke ajiye fitsari mai yawa a uwar dakansu duk da su na da bayi.

Mutumin ya kara da bayyana yadda matarsa ba ta wanke sutturun yaransu.


Kamar yadda ya ce, ta gwammaci ta tsula fitsarinta a daki kuma ta ajiye a dakin, kafin ya kammala magana ta gaura masa mari.


Matar ta ce wulakanta ta ya ke son yi a gidan rediyo wanda jama’a da dama su ke sauraronsu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe