37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Yadda wani bebe ya sanya yaya da ƙanwa suka aure shi cikin ruwan sanyi, bidiyon su ya bayyana

LabaraiYadda wani bebe ya sanya yaya da ƙanwa suka aure shi cikin ruwan sanyi, bidiyon su ya bayyana

Mutane na cewa hankalin mata yafi karkata kan abinda kunnuwan su suka ji, amma wani beben mutum ɗan ƙasar Rwanda ya bayar da mamaki kan yadda cikin ruwan sanyi ya sanya mata biyu suka aure shi.

Mutumin wanda talaka ne da farko ya auri Nabanti Maliya wacce suka haifi yara uku tare. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

A wata hira da Afrimax English ya bayyana cewa ɗaya daga cikin ƴaƴan ya rasu amma sauran sun rayu, inda babba daga ciki mai shekara 20 baya rayuwa a gida sannan ɗayan mai shekara 19 yana rayuwa tare da iyayen sa.

Wata rana kawai sai ƙanwar Nabanti ta zo gidan tace musu aurenta ya mutu, kawai sai suka yanke shawarar su cigaba da rayuwa tare.

Yayi wa ƙanwar matar sa ciki

A maimakon ta koma gida sai ta zo wajen mu. Mijina ya kamu da ƙaunarta sannan yayi mata ciki, sai suka sanar da ni, sai mu ka yanke shawarar mu yi rayuwa tare.

Muna raba komai, tun daga miji, kwanciya da abinci. Muna ƙaunar junan mu sosai.

A cewar Nabanti Maliya

Mutumin mai shekara 52 da iyalin sa na farko da suna rayuwa ne a gidan jinka amma daga baya sun samu kudi sun gida gida a kusa da tafkin Kivu inda suke rayuwa tare gabaɗayan su.

Wasu abubuwan kawai haka ƙaddara ta zo da su sai sun faru. A cewar Petronilla Maliya

Ƴan’uwan sa basu taɓa tunanin zai ƙara aure ba

Ɗan’uwan sa mai suna Sakabe Calvin bai taɓa tunanin cewa ɗan’uwan sa zai ƙara auren wata mata ba, kuma yayi adawa da haɗin gambizar. Abokan su da makwabta suma sun yi mamakin lamarin.

Mutumin da matan sa manomi wanda suke noma kullum sannan su kuma suna kiwon dabbobin gida irin su awakai.

Wawaye ne ke auren soyayya, saboda kudi zan yi aure, Cewar amarya Habiba

A wani labarin na daban kuma, wata marya ta bayyana cewa ita auren kuɗi zata yi saboda wawaye ne kawai ke auren soyayya.

Wata amarya mai suna Habiba Gado ta wallafa hotunanta a Facebook na kafin aurensu ne tare da angonta wanda taken da ta yi wa hotunan ya yi matukar daukar hankulan mutane da dama.

Aure saboda kudi zan yi, babu abinda ya dame ni da shirmenku, a cewarta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe