32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Saurayi ya nemi yafiya wurin budurwarsa da N10m, hotunan sun ɗauki hankula

LabaraiSaurayi ya nemi yafiya wurin budurwarsa da N10m, hotunan sun ɗauki hankula

Wani matashin saurayii ya ja hankulan masu amfani da yanar gizo da hanyar sa ta musamman ta neman yafiya a wurin budurwar sa.

Matashin saurayin yayi wani abin ban mamaki wanda ya ɗauki hankulan mutane kan yadda ya nemi yafiya a wurin budurwar sa bayan ya ɓata mata rai.

Saurayin ya bata makuɗan kuɗaɗe don neman yafiyarta

Matashin saurayin dai ya bayar da tsabar kuɗi har naira miliyan goma, ƴar bebin roba da wasu kyaututtukan na musamman. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

A wasu hotuna da suka karaɗe yanar gizo, kyakkyawar budurwar ta riƙe wani allon rubutu da saurayin nata ya bata. A jikin allon rubutun an rubuta ‘yi hakuri’

Lamarin ya ɗauki hankula sosai, inda mutane da dama suka yi ta magana akai

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su kan lamarin, masu amfani da yanar gizo sun nuna jindaɗin su kan abinda matashin yayi. Yayin da wasu ƴanmatan kuma suka ji dama ace sune abin ya faru da su, wasu kuma sun nuna matuƙar kaduwar su akan lamarin.

Judy Omojody ta rubuta:

Da farko zan so sanin abinda matashin yayi. Saboda wannan kamar ya siye ta da kuɗi ne. Nemi yafiya a wajena irin haka zai sa na damu da sanin ake ɓoye min. Saboda meyasa? Ubangiji nima sai yaushe?

Ya ki hakuri in kile, inji budurwar da saurayinta ya rabu da ita lokacin tana sanya Hijabi

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta bayyana yadda saurayinta ya ƙasa haƙur ta kile, ya rabu da ita saboda tana sanya hijabi.

Wata budurwa wacce musulma ce ta bayyana wa duniya yadda saurayinta ya rabu da ita lokacin tana sanya hijabi inda tace ya kasa hakuri ya kile, Legit.ng ta ruwaito.

A cewarta, saurayinta ya so ta dena sanya hijabi amma ta ki a lokacin, ashe da ya kara mata lokaci da ta waye ta zama daidai da yadda yake so.

Hotunan da Hassanat Abass Abiodun ta wallafa na lokacin tana sanya hijabi sun yi matukar bai wa mutane da dama mamaki.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe