27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Bayan ganin rashin amfaninta a jikin mutum, Gwamnatin Tarayya na son haramta cin ganda

LabaraiBayan ganin rashin amfaninta a jikin mutum, Gwamnatin Tarayya na son haramta cin ganda

Gwamnatin tarayya na yunkurin haramta cin ganda sakamakon ganin rashin amfaninta a jikin dan Adam. Ganda matsayin fatar jikin daban ce don haka gwamnatin ta dakatar da ci, Legit.ng ta ruwaito.

Hakan zai taimaka wurin dakatar da asarar fatun dabbobi kamar yadda Cibiyar Fasahar Najeriya ta Leda ta bayyana.

Duk da dai hakan zai yi matukar bata wa mutane da dama rai musamman masu jindadin morar gandar amma hakan zai yi amfani kawarai kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Farfesa Muhammad Yakubu, darekta janar na Cibiyar NILEST da ke Zaria ya tabbatar da hakan.

Yakubu ya ce wannan matakin na da matukar muhimmanci wurin bunkasa harkar Leda a kasar nan.

Ya ci gaba da bayyana cewa dabi’ar cin fatun dabbobi ba mai kyau bace don ba su da wani amfani a jikin dan adam.

Kamar yadda ya bayyana:

A iyakar sanina, ‘yan Najeriya su ne kadai mutanen da ke amfani da fatun dabbobi a matsayin abinci, ganda ba ta da wani amfani a jikin mutum.”

Labari mai daɗi: Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin ƙara haraji kan ɓangaren sadarwa

Gwamnatin tarayya a Najeriya ta dakatar da shirinta na ƙara yawan harajin da take amsa daga kiran waya, Data da sauran ayyukan sadarwa.

Jaridar Vanguard ta ambato ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami, ya bayyana haka a ranar Litinin, a wurin wani taron ƙaddamar da kwamitin shugaban ƙasa kan harajin aiki na ɓangaren tattalin arziƙin zamani a birnin Abuja.

Ɓangaren sadarwa na fama da yaean haraji kala-kala

Sheikh Pantami yace ɓangaren sadarwa yana fama da yawan haraji kala daban-daban waɗanda suka wuce ƙima.

Sheikh Pantami ya kuma ƙara da cewa a karan kansa baya goyon bayan ƙara yawan harajin, wanda ko tantama babu zai ƙara tsadar kuɗin kiran wayar salula, da mutane ke kashewa.

Tun a baya dai gwamnatin tarayyar ta hannun ofishin kasafin kuɗi na ƙasa ta bayyana cewa zata fara aiki da sabon harajin aikin kan harkokin sadarwa da kayan maƙulashe a shekarar 2023.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe