31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Mufti Ismail Menk ya garzaya Pakistan domin taimakawa mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su

LabaraiMufti Ismail Menk ya garzaya Pakistan domin taimakawa mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su

Sanannen malamin addinin musuluncin nan Mufti Ismail Menk, yanzu haka yana ƙasar Pakistan domin taimakawa mutanen da iftila’in ambaliyar ruwa ta ritsa da su.

Yanzu haka yana a Sindh domin bada agajin gaggawa ga mutanen da mummunar ambaliyar ruwan ta ritsa da su. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

A shafin sa na Instagram, Mufti Menk ya sanya wani bidiyo wanda ya nuna shi yana ziyartar inda ambaliyar ruwan ta shafa a Sindh, Jhuddo.

A wani kira da yayi ga mabiyan sa, Mufti Menk ya roƙe su da su taimakawa mutanen da abin ya ritsa da su.

A wata wasiƙar da ya fitar ya bayyana cewa:

Lamarin ya ta’azzara! Ana buƙatar mu a Pakistan! Ku taimaka da tantuna. Ku taimaka wurin kawo agaji a rayuwar iyalai ta hanyar samar musu da jin ƙai! Akwai tantuna kan farashin £100 kowane! Akwai buƙatar neman agaji nan da wasu shekaru masu zuwa.

Mufti Ismail Menk ya shahara sosai

Mufti Ismail Menk sananne kan fahimtar sa ta koyarwar addinin musulunci. Mufti Ismail Menk yana da sama da mutum miliyan ɗaya masu bibiyar sa a shafin Facebook domin shawarwarin sa kan yin rayuwa mai kyau.

Yana kuma sanya bidiyoyi a Youtube lokaci bayan lokaci kan darussan musulunci da kuma kuma abubuwan dake faruwa da suka shafi musulmai a duniya gabaɗaya.

Mufti Ismail Menk malami ne, mai wa’azi kuma ɗan gwagwarmaya wanda aka haifi a birnin Kaduna a tarayyar Najeriya. Shine kuma ya kafa gidauniyar Islamic Mission Foundation, wacce ke da rassa a sama da ƙasashe 30 a duniya.

Wani mutumi dan kasar Pakistan da ya shafe shekaru 43 yana tara kudin aikin hajji ya rasu a Makka

A wani labarin na daban kuma, wani mutum ɗan ƙasar Pakistan daya kwashe shekaru yana tara kuɗin aikin Hajji ya rasu a Saudiyya.

Zuwa Makkah domin yin aikin Hajji, shi ne burin kowane musulmi. Ga labarin wani mutum da ya dinga tara kudi kusan shekaru 43 domin cikar burinsa na ziyartar dakin Allah.

Ya tara kudinsa tsawon shekaru 43 don yin aikin Hajji. Bai yi kasa a gwiwa ba ya cigaba da tara kudi na tsawon wannan lokaci saboda kwadayin yin aikin Hajji.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe