31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Subhanallahi: Saudiyya za ta bawa al’ummar kasar damar shan giya a wuraren shakatawa

LabaraiSubhanallahi: Saudiyya za ta bawa al'ummar kasar damar shan giya a wuraren shakatawa

Rahotanni sun nuna yadda Saudi Arabia za ta fara yarda da siyar da giya. Kwanannan za a bude mashayar giya iri-iri a wurin wanka na manyan biranen Neom shekara mai zuwa, The Islamic Information ta ruwaito.

Wall Street Journal ce ta ruwaito bayan duba akan takardun ci gaban biranen kasar na wayan Janairun shekara mai zuwa. Kamar yadda takardar ta nuna, za a bude mashayy a wurin Red Sea Island mai suna Sindalah shekara mai zuwa.

A baya, daga sha, shigo da giya har siyar da ita haramun ne a Saudi Arabia. Wadanda su ka karya dokar su na fuskantar hukunci kamar dauri a gidan yari da kuma duka.

Zargin halasta shan giya a Neom ya kara tabbata ne bayan gano batun shirin yin zane da ke nuna ana zuba giya daga kwalba a gaban tsibirin.

Sannan akwai hoto kala-kala a tsibirin Sindalah na watan Yuni wanda ke nuna mata da rigar mama da dan kamfai yayin da maza ke sanye da gajerun wanduna babu Riga jikinsu a gefen ruwan wanka.

Har yanzu dai wakilan Neom ba su riga sun tabbatar da halasta giyar ba. Sannan Sarki Salman bin Abdulaziz al-Saud bai riga ya ce komai ba dangane da lamarin ba.

Sai dai tun watan Mayu ake ta yada batun halasta shan giya a Saudi Arabia. Yanzu haka dai gwamnatin Saudi Arabia ta musanta batun rahotanni dangane da halasta shan giyan a Neom.

A dayan bangaren, shugaban harkokin yawon shakatawa na Neom, Andrew McEvoy, ya ce za su kafa dokokin da za su bayar da dama ga mutanen kasar waje su yi aiki kuma su iya zama a yankin.

Hakan yasa McEvoy ya bukaci a bayar da damar shan giya. Daga bisani gwamnatin Saudi Arabia ta musanta kalaman McEvoy.

Wizkid ya gudanar da ƙayataccen wasan casu a Saudiyya, ya kafa wani babban tarihi

Shahararren mawaƙin ‘Afrobeats’ ɗan Najeriya, Wizkid ya kafa wani tarihi inda ya zama mawaƙi na farko da ya taɓa jagorar wani babban taron wasanni na duniya.

Taron na wasanni wanda yake gudana yanzu haka anyi shi ne a wurin hutawa na NXT LVL Arena, a birnin Riyadh Boulevard na Saudiyya. Jaridar Vanguard ta rahoto.

Mawaƙin wanda ya lashe kyautar Grammy ya gudanar da wasa mai ɗaukar hankali a gaban ɗumbin mutane a wurin shagalin Gamers8 eSports, ranar Alhamis 4 ga watan Agusta, 2022.

Wizkid tare da taimakon maƙaɗin sa, Dj Tunez da ƴan tawagar sa, sun nishaɗantar da mutanen da waƙoƙinsa sabbi da tsofaffi.

Wizkid yayi wasa mai ɗaukar hankalin ƴan kallo

Mawaƙin ya gabatar da wasa mai kyau mai ɗaukar hankali da manyan waƙoƙinsa da suka shahara irin su “Essence”, “Ojuelegba”, ‘Joro’, ‘Come Closer’, ‘Beat Of Life’, ‘Mood’, ‘Ginger’, ‘Soco’ da sauran wasu da dama.

Wannan ƙayataccen taron wasannin da yake gudana a Saudiyya, ana kallon sa a matsayin “babban shirin wasanni na esports na duniya”, inda ake yin wasanni da abubuwan nishaɗi da kuma nuna al’adu.

An fara shine a ranar 14 ga watan Yuli sannan an shirya kammala shi a ranar 8 ga watan Satumba, 2022.

Bikin na Gamers8 ya zo da abubuwan ban nishaɗi, ƙayatarwa ga ɗumbin mahalarta wurin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe