Ministan sadarwa, Farfesa Aliyu Isa Pantami, ya gwangwaje jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi da babban mukami a ma’aikatarsa kamar yadda shafin Kannywood Celebrities su ka bayyana.
Kamar yadda su ka wallafa wata takarda mai dauke da tambarin masana’antar sadarwa, an nuna yadda Ministan ya bai wa jarumin mukamin jakadan ranar NIMC da za ayi ta shekarar 2022/2023.
Kamar yadda takardar ta nuna, dalilin ranar shi ne wayar da kan jama’a dangane da hakkinsu, ayyuka da damar su a tattalin arzikin kasa.
Kuma hakan dama ce wacce za ta nuna ayyukan gwamnati karara dangane da NIMC. Mukamin na shekara daya ne cur kuma zai fara aiki ne a ranar 16 ga watan Satumban 2022 zuwa ranar 15 ga watan Satumban 2023.
Za a iya sabunta nadinsa amma sai an ga yanayin kwazonsa a aikin. Har ila yau, ma’aikatar NIMC za ta iya lokaci bayan lokaci gayyatarsa don wayar da kansa dangane da harkar lambar katin dan kasa da kuma harkoki masu kama da hakan da sauransu.
Mu na taya jarumin murna da fatan Allah ya taya shi riko. Ameen.
Ba mu amince da Farfesan da aka bawa Isah Ali Pantami ba, saboda ya karya doka – Kungiyar ASUU
Hadaddiyar kungiyar malaman jami’oin Nageriya (ASUU) ta ayyana karin matakin karatu da akayi wa Ministan sadarwa Dr. Ali Ibrahim Pantami, a matsayin na bogi. Kuma ya saba da doka.
Kungiyar ta bayyana matsayin farfesan Pantamin cewa na bogine
Kungiyar ta ayyana karin matsayin karatun a matsayin na bogi ne, bayan taron shuwagabannin ta na kasa.
An sanar da hakan ne a wani taron manema labarai wanda shugaban kungiyar Prof. Emmanuel Osodekeya, ya gudanar a ranar Litinin.
Ya ce:
“Ba za ka iya zama minista kuma ka zama Malamin jami’a a lokaci guda ba. Wannan yana daure gindin karya doka.
“Sai dai Pantami ya ajiye mukaminsa na minista sannan yayi kokarin hada aiki biyu a hukumar tarayya. Bai cancanta ba, ba za’a muamalanci Pantami a matsayin farfesa ba”
A watan Satumba na shekarar 2021, jagorancin tuntuba da bada shawara na jami’ar kimiyya da fasaha ta kasa, dake Owerri, suka daga matsayin karatun Pantamin tare da wadansu mutum bakwai 7, zuwa ga matsayin farfesoshi, a karshen taron su na goma sha takwas.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com