Shugabannin majalisar wakilai ta ƙasa tace zata gana da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan yajin aikin ASUU.
Shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila, ya bayyana hakan a ranar Talata bayan saka labule na sa’o’i biyar tare da shugabannin ASUU da ƙaramin ministan ilmi, Goodluck Opiah, a majalisar. Jaridar The Cable ta rahoto.
Ƴan majalisar za su gana da shugaban ƙasar idan ya dawo gida Najeriya, duk da dai ba a saka ranar yin wannan taron ba.
Shugabannin majalisar sun cimma matsaya da malaman jami’a
Da yake magana bayan kammala taron a ranar Talata, Gbajabiamila yace an cimma wasu alƙawura da ASUU.
Akwai abubuwa bakwai da ASUU suka kawo, wanda muke ganin sune abinda zai sa su koma aji.
Mun duba abubuwan nan guda bakwai sannan mun cimma matsaya akan wasu daga ciki.
Zamu gana da shugaban ƙasa domin fayyace masa yarjejeniyar da muka cimma. Muna sa ran shugaba ƙasa zai amince da matsayar da muka cimmawa, wanda a hakan ina da yaƙinin cewa za a kawo ƙarshen matsalar nan.
A halin da ake ciki daga yanzu zuwa lokacin da shugaban ƙasa zai dawo, ASUU za ta je ta tattauna da mambobin ta kan alƙawuran da muka cimmawa.
Shugaban ASUU yayi nasa tsokacin
Da yake nasa jawabin shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodoke, yace zasu tattauna da ƴaƴan ƙungiyar bisa matsayar da aka cimmawa tare da shugabannin majalisar.
Nan gaba kaɗan wannan yajin aikin zai zo ƙarshe
A cewar sa
Yadda na kawo ƙarshen yajin aikin ASUU cikin kwana ɗaya -Goodluck Jonathan
A wani labarin na daban kuma, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan y bayyana yadda ya kawo ƙarshen yajin aikin ASUU cikin kwana ɗaya.
Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana yadda gwamnatin sa ta kawo ƙarshen yajin aikin da ASUU ta shafe wata huɗu tana yi cikin rana ɗaya.
Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, a wurin bikin cikar shekara 70 a duniya na Matthew Hassan Kukah, Bishop ɗin Katolika na Sokoto Diocese, wanda cibiyar Kukah ta shirya.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com