
Gwamnatin jihar Kaduna a ranar Talata ta ce ba za ta amince da tare babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta ke shirin yi a wata zanga-zanga da ta shirya kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i suka tsunduma.
Daliban jami’o’in gwamnati a Najeriya na gudanar da zanga-zanga a wurare mabanbanta a kokarin su na tursasawa gwamnati ta biya bukatar ASUU domin kawo karshen yajin aikin da suka shafe watanni shida shida sunayi.
Daliban a ranar Litinin din da ta gabata a jihar Legas sun toshe hanyoyin zuwa filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA), inda suka hana zirga-zirga a hanyar na tsawon sa’o’i.
Shugaban dalibai NANS reshen jihar Kaduna Dominic Philip, a cikin wata sanarwa, ya yi kira ga mambobin kungiyar da su rufe babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Laraba, don matsawa gwamnati wajen ganin an kawo karshen yajin aikin.
“Game da zanga-zangar da kungiyarmu ta NANS ta ke yi a fadin kasar nan a kudurinta na ganin an janye yajin aikin ASUU, na rubuto ne domin in sanar da ku za mu rufe babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna da ke Gonin Gora ta Kwalejin Cooperative College Kaduna.
“Saboda haka, duk National Excos, Zonal Excos dake Kaduna, JCC Executives, SUG’s/SRC Executives, iyaye masu kishin kasa maza da mata ’yan jarida duk muna gayyatar su zuwa wannan zanga-zanga.
“Dukkan SUGs a jihar su hada motocin su dana kungiyarsu don zuwa wurin taron. Wanda zai gudana Ranar 21 ga watan Satumba, 2022. Da misalin karfe 7 na safe.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com